
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsige Babbar Sakatariyar Cibiyar Inganta Harkar Fansho (PTAD), Dakta Chioma Ejikeme inda ya maye gurbinta da wata matar.
A wata sanarwa da Kakakin PTAD, Olugbenga Ajayi ya fitar, Shugaba Tinubu ya naɗa Mis Tolulope Abiodun Odunaiya a matsayin Shugabar Hukumar Fansho kuma babbar sakatariyar PTAD.
Saidai kakakin ya ce Shugaba Tinubu bai bada bayanin dalilan da suka sa aka tsige Dakta Ejikeme ba watanni 13 bayan sake naɗa ta da ya yi.
Tuni Mis Odunaiya ta kama aiki a ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba, 2024 a Hedikwatar Cibiyar da ke Abuja inda jami’an wajen suka marabce ta ciki girmamawa.
Ta kuma yi alwashin aiki tuƙuru wajen ganin an kiyaye harkokin fansho tare da neman goyon bayan jami’an hukumar.