Wayoyin kamfanin Sin sun yi fice a kasuwannin Afrika a rubu’i na huɗu

Daga CMG HAUSA

Nau’o’in wayoyin hannu na zamani wanda kamfanin Transsion Holdings, na ƙasar Sin ke ƙerawa, sun samu matukar karɓuwa a kasuwannin wayoyin hannu na zamani na Afrika a rubu’i na huɗu na shekarar 2021, inda adadin ya bunƙasa da kashi 47.9 bisa 100, kamar yadda rahoton wani kamfanin ƙasa da ƙasa ya fitar a baya bayan nan.

Alƙaluman da kamfanin na International Data Corporation (IDC) ya fitar ya nuna cewa, kamfanin Transsion, wanda ke ƙera wayoyin Tecno, Infinix, da Itel, ya sha gaban kamfanonin Samsung da Xiaomi (da kuma Poco) da kashi 19.6 da kuma kashi 7.1 bisa 100.

Taher Abdel-Hameed, babban mai sharhi kan bincike na kamfanin IDC ya ce, ƙarancin wayoyin hannu a kasuwannin duniya, da matsin lambar tsadar farashi, da ingantattun gilasan fuskokin wayoyin, da kuma ingancinsu, na daga cikin dalilan da suka sanya tsadar farashin wayoyin hannu na zamani.

IDC ya ce, a shekarar 2022 yana sa ran kasuwar wayoyin hannu ta zamani ta Afrika za ta bunƙasa da kashi 3.8 bisa 100 a bisa na makamancin lokacin bara.

Fassarawa: Ahmad Hassan