Wike ya ƙwace filaye 568 ciki har da na Buhari da na Kakakin Majalisar Wakilai a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Abuja Nyesom Wike ya ƙwace kimanin filaye 568 a babban birnin bisa rashin biyan kuɗaɗen ƙa’ida na shaidar mallaka ta CofO.

Daga cikin su akwai na Gidauniyar tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, na Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, na Gwamnonin Jihohin Bayelsa da Imo, Sanata Diri Douye da Sanata Hope Uzodimma; sai na jagoran sanatoci Opeyemi Bamidele da kuma na Sakataren jami’iyyar PDP na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu.

Sauran a jaddawalin sun haɗa da na tsohon gwamnan Enugu, Chimaroke Nnamani; Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Abba Moro; Shugaban NiDCOM, Hon. Abike Dabiri-Erewa; ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Obokun/Oriade, Hon. Oluwole Oke da sauran su.