
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya amince da karɓe ikon mallakar filaye guda 4,794 bisa rashin biyan kuɗin hayar ƙasa na tsawon shekaru 40.
Blueprint ta ruwaito cewa, a yankin Central Area da Garki na 1 da na 2 da Wuse na 1 da na 2 da Asokoro da Maitama da Guzape, kimanin masu filaye 8,375 ne ba su biya kuɗin hayar ba a tsawon shekaru 43.
A wani taron bita ga manema labarai da babban mai taimaka wa ministan kan yaɗa labarai, Lere Olayinka da Daraktan Filaye na Abuja, Chijioke Nwankoeze, suka bayyana hakan inda suka ce a baya an yi ta sanarwar gargaɗi game da biyan kuɗaɗen hayar ga masu filayen ta kafafen labarai.
Sun ce, duk da haka ba a samu adadi mai yawa na waɗanda suka amsa kiran ba, wanda faro tun a shekarar 2023.
An dai tsara filayen waɗanda suka gaza biyan kuɗaɗen a tsofaffin gundumomi goma na zangon farko a Abuja. Ga su kamar yadda Blueprint ta ruwaito; Central Area District (Cadastral Zone A00), Garki I (Cadastral Zone A01), Wuse I (Cadastral Zone A02), Garki II (Cadastral Zone A03), Asokoro (Cadastral Zone A04), Maitama (Cadastral Zone A05), Maitama (Cadastral Zone A06), Wuse II (Cadastral Zone A07), Wuse II (Cadastral Zone A08) and Guzape (Cadastral Zone A09).
Haka kuma, zuwa ƙarshen 2024 har zuwa yau, aƙalla N6,967,980,119 ake bin masu fili guda 8,375 a birnin, wanda hakan ke nuna sama da shekara ɗaya kenan ba su biya ba.
Masu fili guda 4,794 da aka ƙwace, sun kai kimanin shekaru goma ba su biya kuɗin hayarsu ba a gundumomin da aka lissafo.