A wani mataki na yin aiki ba sani ba sabo da Ministan Abuja, Nyesom Wike, yake yi don gyara wa birnin tarayya zama, Ministan ya ƙwace wasu filaye a birnin mallakar ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyya Labour (LP) a babban zaɓen 2023, Peter Obi da tsohon Gwamnan Kuros Riba Liyel Imoke.
Sanarwar da Babban Sakataren Hukumar Abuja, Olusade Adesola, ya fitar a ranar Alhamis ta nuna filayen Obi da na Imoke na daga cikin fuloti 165 da ministan ya janye mallakarsu ta dawo hannun gwamnati.
A cewar sanarwar, Wike ya ƙwace filayen ne sakamakon mamallakansu sun ƙi gina su.
“Hukumar Abuja na sanar da al’umma cewa, Ministan Abuja a bisa ikon da Sashe na 28(5)(a) da (b) na Dokar Fili ta 1978 ya sahale masa, ya janye mallakar filayen da aka lissafa kamar yadda yake a cikin bayananmu saboda rashin gina su da ba a yi ba,” in ji sanarwar.
Baya ga Obi da Imoke, sauran waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da tsohon Ministan Tsare-tsare na Ƙasa, Udo Udoma, tsohuwar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ufot Ekaette, taohon Sanatan Edo ta Arewa, Victor Oyofo, mamallakon kamfanin jaridar Leadership, marigayi Sam Nda-Isaiah da sauransu.