
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ƙwace filin Sakatariyar jam’iyyar PDP ta ƙasa dake Central Area a Abuja.
Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan Filaye na Abuja, Chijioke Nwankoeze, inda ya ce ya yi hakan ne saboda jam’iyyar adawar ba ta biya kuɗin hayar ƙasa ba na tsawon shekaru 20.
Daga ranar 1 ga watan Junairun 2006 zuwa 1 ga watan Junairun 2025 ne PDP ba ta biya kuɗaɗen ƙa’idar ba duk da cewa an yi ta sanarwa a kafafen watsa labarai na tsawon lokaci.
Ya kuma ce, daga yanzu Hukumar Raya Birnin Abuja, (FCTA), za ta cigaba da jan ragamar filin har sai an biya baki ɗaya kuɗaɗen kafin a mayar masu.