Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya kafa wani kwamiti don kula da batun almajirai a cikin babban birnin.
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Olatunji Disu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan wani taron tsaro na sirri da ministan babban birnin tarayya ya jagoranta.
Ya bayyana cewa, ministan ya ɗauki wannan mataki ne don tabbatar da cewa hukumomin tsaro suna da cikakkun bayanai na almajirai musamman ayyukansu da suka haɗa da walwalarau da ayyukan makaranta.
Ko da yake ya yi watsi da tambayoyin da suka shafi barazanar tsaro a babban birnin ƙasar, Disu ya yi kira ga mazauna yankin da su kasance masu lura da tsaro tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga hukumomin tsaro.
Kwamitin wanda ya haɗa da ‘yan sandan Nujeriya da jami’an tsaro na Sibil Difens, DSS da dai sauransu an umurce su da su gabatar da rahoto cikin makonni biyu.
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa rundunar ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.