Wike ya sha alwashin gurfanar da ɓarayin murafun magudanan ruwan Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya sha alwashin gurfanar da mutane 50 da ake tsare da su bisa laifin sace murafun magudanan ruwan titunan Abuja.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, a ranar Litinin ɗin da ta gabata, rundunar ‘yan sandan Nijeriya a babban birnin tarayya Abuja ta sanar da tsare wasu mutane 50 da ake zargi da aikata ɓarna, waɗanda aka kama da murafai 25 da fitilun tituna masu amfani da hasken rana.

Da yake mayar da martani game da lamarin, Wike ya ce waɗanda ake zargin za su fuskanci fushin doka don zama izina ga wasu.

A wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin sadarwa da sabbin kafafen yaɗa labarai, Lere Olayinka, ministan ya jaddada cewa babu wani mai laifi da zai tsira.

Ya kuma bada tabbacin cewa hukumar babban birnin tarayya Abuja za ta tabbatar da cewa duk masu saye da masu amfani da murafen da aka sace da sauran ababen more rayuwa na jama’a za su fuskanci hukunci.

Masu laifin, ya ce za a gurfanar da su gaban kuliya bisa laifin zagon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasar da kuma jefa rayuwar ‘yan Nijeriya cikin haɗari.

Wike ya bayyana tsare mutanen 50 da ake zargi da aikata ɓarna a matsayin nuni da manufar daƙile aikata laifi ta hukumar FCTA, musamman ɓarnatar da ababen more rayuwa.

Ya yaba wa hukumomin tsaro bisa gaggarumin matakin da suka ɗauka, yana mai kiran ƙoƙarin haɗin gwiwarsu da “abin yabo”.

“Wannan tabbaci ne ga mazauna FCT cewa rayukan su da dukiyoyinsu suna cikin tsaro,” inji shi.

Ministan ya kuma yaba wa ‘yan Nijeriya kan yadda suke nuna kishin ƙasa ta hanyar nuna rashin amincewarsu da barna, tare da jaddada cewa kare ababen more rayuwa wani nauyi ne na haɗin gwiwa.

Ya buƙaci mazauna babban birnin tarayya Abuja da su ci gaba da amfani da kafafen sada zumunta yadda ya kamata, kamar yadda wani mutum ya sanar da hukuma game da sace-sacen.

Ya yi alƙawarin cewa hukumar za ta yi gaggawar magance irin wannan lamari a nan gaba.