WOMFOI za ta tallafa wa mata don shiga harkokin siyasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Ƙungiyar ‘Women Mentoring and Leadership Initiative’ (WOMFOI) ta karrama ƙungiyar haɗin gwiwa, don yin gyara da koyo (PERL), saboda tallafa wa mata da su shiga harkokin siyasa a jihar Kaduna.

PERL wani shiri ne na tsarin mulki na Ofishin Harkokin Waje na Birtaniya, yana aiki don ƙarfafa tsarin mulki da inganta ayyukan ’yan ƙasa a cikin tafiyar da mulki.

Shugabar ƙungiyar, Misis Florence Aya, ta ba wa PERL lambar yabo a Kaduna ranar Laraba, yayin wata ganawa da ƙungiyoyin ’yan ƙasa, mata, da ’yan jarida.

Ƙungiyar PERL ce ta shirya taron domin jan hankalin ƙungiyoyin ’yan ƙasa, mata, da kafafen yaɗa labarai domin tsara ajandar zaɓen 2023.

Aya ta ce, wannan karramawar ta kasance ne don nuna godiya ga kyakkyawan goyon baya da sadaukarwar da PERL ke bayarwa wajen bunƙasa da cigaban ƙungiyar ta WOMFOI.

Ta ƙara da cewa, tallafin da ƙungiyar ta PERL ta bayar ya gina ƙwarin gwiwar mata a harkokin siyasa da kuma yadda mata za su iya shiga harkokin siyasa yadda ya kamata.

A cewarta, PERL ta shawarci ƙungiyar mata kan yadda za su yi burin kowane muƙami na siyasa, yadda za a rubuta takarda, yadda za a samo kuɗaɗe, da kuma yadda za a samar da tallafi.

“Hakazalika, PERL ta horar da mu kan bayar da shawarwari masu inganci, yin magana da jama’a da yadda ake amfani da kafafen yaɗa labarai wajen samar da talla da wayar da kan jama’a da ake buƙata domin gudanar da zaɓen mazaɓu.

“Muna sanin abubuwan al’ajabinmu kuma PERL na ɗaya daga cikinsu saboda shirin gwamnati ya tallafa mana tun daga farko har zuwa yau.

Aya ta ce, manufar WOMFOI ita ce samar da dandali mai ɗorewa da za ta shirya mata jagoranci mai nagarta da kuma ba su damar yin burin kowane matsayi na jagoranci.

Da ya ke mayar da martani, Mista Adejor Abel, Malami na ƙungiyar ta PERL, wanda ya samu lambar yabo, ya gode wa ƙungiyar mata bisa karramawar, inda ya bayyana ta a matsayin ‘karramawa ta gaskiya’.

“Muna matuƙar godiya da wannan karramawar da muka samu daga ƙungiyoyin mata a jihar Kaduna domin taimaka musu wajen gudanar da harkokin siyasa yadda ya kamata da kuma fafutukar neman muqamai da zaɓe.

“PERL za ta cigaba da zaburar da mata don su shiga cikin fagen siyasa don a ji muryoyinsu da kuma shiga cikin tsarin yanke shawara a jihar,” inji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, tsarin kula da harkokin ƙananan hukumomi na Kaduna (LGAM), wani tsarin nuna gaskiya, da tabbatar da al’amuran ƙananan hukumomi shi ma ya bayar da lambar yabo ga PERL kwanan nan.
Wannan karramawar a cewar ƙungiyar, ita ce nuna godiya ga goyon bayan da PERL ke bayarwa na sake fasalin ƙananan hukumomi da kafa ƙaramar hukumar a ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Unguwar ta kuma yi na’am da irin gagarumar gudunmawar da PERL ke bayarwa wajen inganta ƙungiyoyin jama’a (CSOs) wajen tafiyar da harkokin mulki, tabbatar da kyakkyawan shugabanci da samar da ingantacciyar hidima.