Xherdan Shaqiri ya zama ɗan wasa mafi yawan albashi a MLS ta Amurka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu bayanai na nuna cewa ɗan wasan gaba na Switzerland Xherdan Shaqiri shi ne ɗan wasa mafi ɗaukar albashi a Lig ɗin MLS da ke Amurka.

Bayanan da aka fitar a ranar Talata sun nuna cewa, Shaqiri da ke taka leda da Chicago Fire na ɗaukar albashin dala miliyan 8 da rabi yayin da Lorenzo Insigne da ke taka leda da Toronto ke ɗaukar albashin dala miliyan 7 da rabi kana Javier Hernandez na Los Angeles Galaxy a matsayin na 3 da albashin dala miliyan 7.

Shaqiri mai shekaru 31 wanda ya taka leda da ƙungiyoyin Turai da dama da suka ƙunshi Bayern Munich ta jamus da Inter Milan ta Italiya da kuma Liverpool ta Ingila baya ga Lyon ta Faransa ya zura ƙwallaye 7 a wasanni 35 da ya dokawa Chicago fire cikin wannan kaka.

Galibi ‘yan wasan da suka rasa cikakkiyar dama a Turai ko kuma waɗanda tauraruwarsu ta daina haskawa kan je ƙasashe irin Amurka da China da Turkiya da Saudiya waɗanda ke biyan ‘yan ƙwallo maƙuden kuɗaɗe.