Xi Jinping: Sin na goyon bayan shigar da ƙungiyar AU G20

Daga MARYAM YANG

Cikin jawabin da ya gabatar a yayin zaman farko na taron ƙolin G20, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, ƙasar Sin tana goyon bayan shigar da ƙungiyar tarayyar ƙasashen Afirka wato AU cikin ƙungiyar G20.

Ya ce, a halin yanzu, ƙasashen duniya, musamman ma ƙasashe masu tasowa suna fuskantar ƙalubalen raguwar tattalin arziki. Don haka ya ba da shawarar kafa dangantakar abokantaka ta neman farfaɗo da tattalin arzikin duniya, da mai da aikin neman ci gaba, da raya al’umma a matsayin babban aikin da aka sanya gaba, tare da mai da hankali kan buƙatun ƙasashe maso tasowa.

Da safiyar ranar 15 ga wata ne aka buɗe zaman farko na taron ƙolin G20 a tsibirin Bali na ƙasar Indonesiya.

Da safiyar ranar 15 ga wata ne aka buɗe zaman farko na taron kolin G20, a tsibirin Bali na ƙasar Indonesiya, kuma shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya halarci taron, ya kuma gabatar da jawabi.

Kungiyar G20 na fuskantar ƙalubaloli masu tsanani idan aka kwatanta da sauran lokuta a tarihi, a matsayin wani dandalin dake tara manyan ƙasashe da dama, kuma muhimmin dandali ne na haɗin kan ƙasa da ƙasa. Xi Jinping ya sake bayyana matsayin Sin kan manufofin da ta gabatar, yana mai kira ga sauran ƙasashe da su amince da ra’ayin kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai ɗaya, da haɗa kai don samun ci gaba da moriya, tare da yin haƙuri da juna, da taimakawa juna a maimakon kawo baraka, da yin fito-na-fito da nuna bambanci, ta yadda duniya za ta samu bunƙasuwa mai ɗorewa.

A jawabin nasa Xi Jinping ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar babban kalubalen raya ƙasashen duniya. Don haka ya kamata mambobin G20 su sauke nauyin dake bisa wuyansu a matsayinsu na manyan ƙasashen duniya, domin neman bunƙasuwar ƙasa da ƙasa, da tallafawa al’ummun duniya, yayin da ake tabbatar da ci gaban duniya baki ɗaya.

Shugaban ƙasar, Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa a tsibirin Bali

Haka kuma, cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata a nemi ci gaban da kowace ƙasa za ta iya cin gajiyar sa. Ci gaban da kowace ƙasa za ta ci gajiya tare, haƙiƙanin ci gaba ne da ake buƙata. Ya kamata ƙasashen dake kan gaba wajen samun ci gaba, su ba da taimako yadda ya kamata ga sauran ƙasashe, da kuma samar musu ƙarin damammakin da suke buƙata.

Ya ce, ƙalubaloli masu tsanani da ake fuskanta wajen neman bunƙasuwar ƙasashen duniya, su ne ƙarancin isasshen hatsi da makamashi. Kuma, muhimmiyar hanyar da za mu yi amfani da ita wajen shawo kan waɗannan ƙalubaloli ita ce, yin hadin gwiwa kan aikin sanya ido a kasuwanni, da kuma kafa manyan kasuwannin buɗe kofa ga waje, domin ƙarfafa tsarin samar da kayayyaki cikin haɗin gwiwa, da kuma daidaita farashin kayayyaki yadda ya kamata.

Bugu da ƙari, Xi Jinping ya ce, a yayin babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta Ƙasar Sin karo na 20 da aka yi watan jiya, an tabbatar da burin ci gaban ƙasar Sin da na JKS cikin shekaru 5 masu zuwa. Kuma ƙasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen neman bunƙasuwa cikin lumana, da zurfafa aikin kwaskwarima, da kuma ƙara buɗe ƙofa ga waje, domin neman farfaɗowar ƙasar Sin baki ɗaya ta hanyar zamanintar da ƙasar.

Shugaban ƙasar Sin, Xi Jinping ya gana da takwaransa na ƙasar Senegal, Macky Sall a tsibirin Bali

Haka kuma, a yayin ziyararsa a tsibirin Bali, shugaba Xi Jinping ya gana da takwaransa na ƙasar Amurka Joe Biden.

Dangane da ganawarsu, mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen ƙasar Sin, Wang Yi ya bayyana cewa, ganawar shugabannin biyu na da muhimmiyar ma’ana, domin wannan shi ne karo na farko da shugaban ƙasar Sin da na Amurka suka yi ganawa fuska ta fuska cikin shekaru 3 da suka gabata, kuma karo na farko da shugabannin biyu suka gana da juna fuska ta fuska, bayan shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya kama aiki.

Kaza lika, wannan shi ne karo na farko, da shugabannin koli na ƙasar Sin da na Amurka suka yi mu’amala, bayan sun kammala muhimman taruka cikin ƙasashensu.

Kana, a yayin ganawar shugabannin biyu, an tabbatar da cewa, za a magance taɓarɓarewar dangantaka a tsakanin ƙasashen biyu, yayin da ake neman wata hanyar da ta dace ta daidaita dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Shugaban ƙasar Sin, Xi Jinping ya gana da takwaransa na ƙasar Amurka, Joe Biden a tsibirin Bali

Kuma, za a tattauna cikin haɗin gwiwa, domin fidda manufar daidaita dangantaka tsakanin ƙasashen biyu. Sa’an nan kuma, an fara yunƙurin aiwatar da ra’ayin shugabannin biyu, ta yadda za a daidaita dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu cikin yanayin zaman karko.

Haka kuma, a yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun mai da hankali kan batun lardin Taiwan na ƙasar Sin. Wang Yi ya ce, ƙasar Sin na fatan Amurka za ta aiwatar da matakai masu nasaba da hakan, kamar yadda ta bayyana, da kuma bin manufar “ƙasar Sin ƙasa ɗaya tak a duniya”, da sanarwar haɗin gwiwa guda uku da ƙasar Sin da Amurka suka ƙulla, da kaucewa ɓata yanayin lardin Taiwan.


Dangane da wannan batu, shugaba Biden ya ce, ƙasar Amurka tana tsayawa tsayin daka kan manufar “ƙasar Sin ƙasa daya tak a duniya”, kuma ba ta goyon bayan ɓallewar yankin Taiwan daga ƙasar Sin, kana kasar Amurka ba ta da burin hana bunƙasuwar ƙasar Sin ta hanyar rura wutar batun Taiwan.

Dangane da ci gaban da ƙasashen biyu suka samu a fannin haɓaka hadin gwiwa bisa fannoni daban daban, shugaba Xi Jinping ya ce, bai kamata a dakatar da aikin raya dangantaka a tsakanin ƙasar Sin da ƙasar Amurka sakamakon bambancinsu ba, kuma ya kamata ƙasashen biyu su duƙufa wajen tsawaita jerin hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Bugu da kari, a yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya bayyana matsayin ƙasar Sin kan wasu batutuwan dake janyo hankulan ƙasar Amurka, da ma sauran ƙasashen duniya. Shugabannin biyu, sun kuma yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan dake shafar ƙasar Ukraine, da batun nukiliyar zirin Koriya da dai sauransu.

Da yammacin ranar 17 ga wata, shugaban ƙasar Sin, Xi Jinping da uwargidansa, Farfesa Peng Liyuan sun isa birnin Bangkok na ƙasar

AEPC ta kasance dandali mai muhimmanci ta fannin haɗin kan tattalin arziki a yankin Asiya da Pacific. A yayin taron APEC da aka buɗe a ranar 18 ga wata, Xi Jinping ya yi cikakken bayani kan dabarun da suka kai ga nasarar da aka samu a fannin tattalin arziki tsakanin ƙasashen Asiya da Pacific.

A cewarsa, bai kamata ƙasashe masu ƙarfi su riƙa yin takara a wannan yankin ba. Kuma ya yi kira da a martaba hanyar samun bunƙasuwa cikin lumana, da yin haƙuri da juna, da bude kofa da zurfafa amincewa da juna, da haɗin kai da samun moriya tare a tsakanin ƙasashen wannan yankin, da kafa kyakkyawar makomar yanki ta bai daya yadda ya kamata. Xi Jinping ya kuma sanar da cewa, ƙasar Sin ta shirya karbar baƙuncin dandalin koli na haɗin gwiwar ƙasashe bisa shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” karo na 3 a badi.

Cikin jawabin da ya gabatar, a yayin ƙwarya-ƙwaryar taron shugabannin ƙungiyar APEC karo na 29, Xi Jinping ya ce, ya kamata a tabbatar da adalci a duniya, da gina yankin Asiya-Pacific mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, kana ya yi kira ga ɓangarori daban daban su gina makoma ta bai ɗaya ta Asiya-Pacific tare, da kuma samun sabuwar nasara a kan haɗin gwiwar yankin.

Xi Jinping ya jadadda cewa, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan buɗe ƙofa da gina Asiya-Pacific inda jama’a za su sami wadata tare. Ya ce a shekarar badi, ɓangaren Sin zai yi tunanin gudanar da dandalin tattaunawar ƙoli na hadin gwiwar duniya kan shawarar “ziri ɗaya da hanya daya”, ta yadda za a samar da sabon kuzari ga neman ci gaba, da samun nasarori a yankin Asiya-Pacific da ma duniya baki ɗaya.

Xi Jinping ya ce, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan samun ci gaba ta hanyar kiyaye muhalli, da gina Asiya-Pacific mai tsabta da kyan gani. Yana mai cewa, ɓangaren Sin zai bayar da goyon baya don cimma makasudin Bangkok, tare da maraba da ƙasashen Asiya-Pacific su shiga cikin ajandar ci gaban ƙasa da ƙasa.

An yi taron kolin APEC karo na 29 a cibiyar taron ƙasa ta Sarauniyar Sirikit a birnin Bangkok na ƙasar Thailand

Har ila yau, Xi Jinping ya bayyana cewa, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan samar da makoma ta bai daya, da gina yankin Asiya-Pacific ta yadda za a rika taimakawa juna. Kuma ya kamata a dage wajen kiyaye manufofin ƙungiyar APEC, da ƙarfafa hulɗar abokantaka ta aminci da haƙuri da juna da haɗin gwiwa da samun nasara tare.

Bugu da ƙari, ya ce, Sin za ta dage tare da ƙara buɗe ƙofarta ga ƙasashen waje, cikin fage mai faɗi da zurfi, da nacewa bin hanyar zamanintarwa irin na kasar Sin, da gina babban sabon tsarin tattalin arziki mai buɗe ƙofa, da samar da ci gaba da yayata gogewarta na ci gaba ga duniya musamman ma Asiya-Pacific.

Daga ranar 14 zuwa 19 ga wannan wata, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ƙolin G20 karo na 17 da aka yi a tsibirin Bali na ƙasar Indonesiya, da taron kolin APEC karo na 29 da aka shirya a Bangkok na ƙasar Thailand. (Maryam Yang)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *