Xi Jinping ya ƙarfafa wa ɗaliban jami’a gwiwar koyon ilmin malanta don taimaka wa yankuna masu ƙarancin cigaba

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya amsa wasiƙar da ɗaliban jami’ar horar da malamai ta Beijing suka rubuta masa a jiya Laraba, ɗaliban da suke koyon ilmin malanta don tallafa wa yankuna masu ƙarancin ci gaba dake yankin tsakiya da yammacin ƙasar.

Shugaba Xi ya yi musu kyakkyawar fata yayin da ake bikin cika shekaru 120 da kafuwar jami’ar da ranar malamai karo na 38, inda shugaba Xi ya yiwa dukkanin malamai a ƙasar fatan alheri.

A cikin wasiƙar da ya rubutawa waɗannan ɗalibai, shugaba Xi ya ce, tun lokacin da kuka shiga makarantar shekara guda, kun kara iliminku, da fadada hangen nesa, da ƙarfafa imaninku kan koyarwa da ilimantar da jama’a daga tushe ta hanyar nazarin azuzuwa da aikin koyarwa na sa kai, ina murna sosai.

Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya ce, ina fatan za ku ƙara ƙaimi wajen fadakar da jama’a, koyarwa, da warware dambarwa, bayan kammala karatunku, kana za ku shiga inda jama’a suka fi buƙata, da ƙoƙarin zama malami na-gari.

Mai fassara: Amina Xu