Xi Jinping ya aike da saƙon murna ga bikin tunawa da ranar zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa

Daga CMG HAUSA

An yi bikin tunawa da ranar zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa ta bana a yau Laraba a nan birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin, bikin da ya samu saƙon murna daga shugaban ƙasar Sin Xi Jinping.

Xi ya bayyana cewa, yanayin tsaron duniya na fuskantar manyan sauye-sauye a halin yanzu, kuma duniya ta shiga wani sabon lokaci na sauye-sauye, inda ya fitar da shawarar tsaron duk duniya, da yin kira ga ƙasa da ƙasa, da su tsaya ga ra’ayin tsaro na bai ɗaya, cikin hadin-gwiwa kuma mai ɗorewa, da mutunta ‘yancin kai, da cikakkun yankuna na kowace ƙasa, da girmama kundin tsarin mulkin Majalisar Ɗinkin Duniya, da maida hankali kan damuwar ƙasa da ƙasa.

Haka kuma, Xi ya yi kira a daidaita rikici da sabanin ra’ayi tsakanin ƙasashe ta hanyar yin shawarwari, da ɗaukar nauyin shimfida zaman lafiya, da bin tafarkin samar da ci gaba cikin lumana, a wani kokari na raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai ɗaya.

Mai fassara: Murtala Zhang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *