Xi Jinping ya aike da saƙon taya murna ga zaɓaɓɓen shugaban Kenya

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da saƙon taya murna ga zababben shugaban ƙasar Kenya William Ruto a yau Laraba.

Cikin saƙon, shugaba Xi ya ce, Sin da Keyan na da daddadiyyar alaƙar abota da haɗin gwiwa a ɓangarori da dama, waɗanda suka haifar da kyawawan sakamako a shekarun baya-bayan nan.

Ya ce yana ba ci gaban hulɗarsu muhimmanci, kuma a shirye yake ya haɗa hannu da shugaba Ruto, wajen ɗaukaka huldar zuwa wani muhimmin matsayi domin moriyar ƙasashen biyu da al’ummominsu.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha