Xi Jinping ya gabatar da jawabi ga taron “taimaka wa ƙasashen waje a fannin bunƙasa noman shinkafa mai aure da samar da isasshen abinci na duniya”

Daga CMG HAUSA

A yau Asabar 12 ga wata, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da rubutaccen jawabi, ga dandalin tattaunawar ƙasa da ƙasa kan “Taimakawa ƙasashen waje a fannin noman shinkafa mai aure, da kuma samar da isasshen abinci na duniya”.

A yayin jawabinsa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, samar da isasshen abinci, muhimmin batu ne da ya shafi rayuwar bil’adama.

Ya ce kimanin rabin ƙarni da ya gabata, an samu nasarar yin nazari, da samar da shinkafa mai aure tare da yayata fasahar a ƙasar Sin, wanda hakan ya taimaka wa ƙasar Sin wajen amfani da ƙasa da kashi 9% na filayen noma a duniya, don warware matsalar abinci ga kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, kuma ta zama ƙasa mafi girma wajen noman hatsi a duniya, kuma ƙasa ta uku wajen fitar da hatsi.

Tun daga shekarar 1979, shinkafa mai aure ta bazu, zuwa kusan kasashe 70 dake nahiyoyin duniya biyar, inda ta ba da gudummawa sosai wajen habaka noman hatsi, da raya aikin gona a ƙasashe daban-daban, da samar da irin wannan hanya da ta ɗauka ta warware matsalar ƙarancin abinci ga ƙasashe masu tasowa.

Xi Jinping ya jaddada cewa, ƙasar Sin tana son yin ƙoƙari tare da ƙasashe daban daban, wajen ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin samar da abinci da rage radadin talauci, da ba da gudummawa sosai wajen gaggauta aiwatar da ajandar samun ci gaba mai ɗorewa na MƊD kafin shekarar 2030, da gina duniyar da za ta kuɓuta daga yunwa da talauci.

Mai fassara: Bilkisu Xin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *