Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin bikin cika shekaru 25 da dawowar HK ƙasar Sin da na ƙaddamar da sabuwar gwamnatin yankin

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin ya gabatar da jawabi a taron bikin murnar cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong ƙarƙashin Jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin da kuma bikin ƙaddamar da sabuwar gwamnatin yankin ta 6.

Xi Jinping, wanda shi ne shugaban kwamitin koli na JKS, kuma shugaban rundunar sojin ƙasar, ya taya John Lee, sabon jami’in farko na gwamnatin yankin da manyan jami’ai da mambobin majalisar zartarwar sabuwar gwamnatin yankin murna.

Shugaban ya ce aiwatar da manufar “Ƙasa Ɗaya Mai Tsarin Mulki Biyu” ta haifar da nasarorin da kowa ke iya gani a yankin HK. Kuma tun bayan dawowarsa ƙarƙashin ƙasar Sin, yankin ya bayar da gagarumar gudunmawa ga bunƙasar tattalin arzikin ƙasar mai dogon zango cikin sauri da kuzari ba tare da tangarda ba.

Haka kuma, HK ya zama wani muhimmin bangare ga ci gaban kasar Sin, wanda ya yi daidai da dabarun raya kasar. Baya ga haka, ya ci gaba da rike matsayinsa na mai karfi da bayar da ’yanci da bude kofarsa, tare kuma da kiyaye dokokin kasa da kasa.

Bugu da ƙari, shugaba Xi ya ce, yankin HK ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa sabon fagen fadada da zurfafa manufar bude kofa ta ƙasar Sin a ƙarin ɓangarori.

Kana, HK ya zama jigon saurin ci gaban ɓangaren kimiyya da fasaha da ƙirƙire ƙirƙire, haka kuma ya samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da ya kai mizanin ƙasa da ƙasa.

Har ila yau, ya ce, an kare tare da kyautata dokokin da ake amfani da su a yankin, kuma al’ummarsa sun kasance tsintsiya madaurinki ɗaya.

A cewarsa, tsarin demokraɗiyyar HK da ya dace da manufar “Ƙasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu”, da kundin tsarin mulkin yankin, shi ne mafi dacewa wajen kare haƙƙoƙin demokraɗiyya na mazauna yankin da kuma tabbatar da ci gaba da kwanciyar hankalinsa.

Ya ce manufar “Ƙasa Ɗaya Mai Tsarin Mulki Biyu”, abu ne da aka ga alfanunsa cikin lokaci mai tsawo, don haka babu dalilin sauya ingantaccen tsari irinsa, haka kuma, dole ne a ci gaba da rungumarsa.

Ban da wannan kuma, jami’an sabon gwamnatin yankin sun yi rantsuwar kama aikinsu a bikin.

Fassarawar Fa’iza Mustapha