Daga CMG HAUSA
Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan tawagar rukunin da suka yi aikin ƙera babban jirgin saman fasinja ƙirar C919 a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, kana ya halarci bikin nune-nunen nasarorin da aka cimma, inda ya yaba da nasarorin da aka samu game da aikin ƙera jirgin saman.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, shawagin babban jirgin sama ƙirar ƙasar Sin a sararin sama, shi ne burin ƙasa da al’ummar Sinawa da kuma jama’ar Sin.
Ya ce ya kamata a yi amfani da fifikon sabon tsarin albarkatun ƙasar, da martaba ƙa’idojin tabbatar da tsaro da inganci daga farko zuwa ƙarshe a kan aikin, da kara samun ci gaba kan muhimman fasahohi daga aikin, da kuma gaggauta raya wannan sha’ani da raya ƙasar mai ƙarfin masana’antu.
Babban jirgin saman samfurin C919, shi ne jirgin sama na farko da ƙasar Sin ta ƙera da kanta bisa ma’aunin zirga-zirgar jiragen sama na duniya, wanda ke da ikon mallakar fasaha mai zaman kansa.
An fara aikin nazarin kera jirgin saman ne a shekarar 2007, kuma jirgin ya yi gwajin tashi na farko a shekarar 2017, inda ya kammala dukkan bincike da samun takardar iznin yin zirga-zirga ta ƙasar Sin a watan Satumba na shekarar 2022.
A ƙarshen shekarar 2022 ne, jirgin zai fara shiga kasuwa.
Mai fassara: Zainab