Xi Jinping ya taya murnar ƙaddamar da makarantar Julius Nyerere Leadership dake Tanzaniya

Daga CRI HAUSA

Yau Laraba ne aka gudanar da bikin ƙaddamar da makarantar Julius Nyerere leadership dake ƙasar Tanzaniya, inda babban sakatare na kwamitin ƙolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da saƙon taya murna.

Xi ya jaddada cewa, duniya na fuskantar manyan sauye-sauye a halin yanzu, kuma Sin da nahiyar Afirka na ƙara buƙatar zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya fiye da kowane lokaci da ya gabata, da tinkarar ƙalubaloli, da samar da ci gaba da alheri ga al’umma.

Ya ce jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, tana son yin amfani da wannan dama, don inganta mu’amala tare da jam’iyyun siyasar ƙasashen Afirka daban-daban, da marawa juna baya, wajen neman samar da ci gaba bisa halin da ake ciki a ƙasashe daban-daban, da zurfafa haɗin-gwiwa, da kyautata raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai ɗaya, a wani ƙoƙari na ƙara bayar da gudummawa, ta raya duniya mai kyau.

Fassarawa: Murtala Zhang