Xi Jinping ya zanta da takwaransa na ƙasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho

Daga CRI HAUSA

A yau Juma’a ne shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na ƙasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho. Yayin zantawar, Xi Jinping ya sake godewa Putin, bisa zuwan sa ƙasar Sin don halartar bikin buɗe gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi ta birnin Beijing, ya kuma taya ‘yan wasan ƙasar Rasha murnar samun matsayi na biyu a jerin lambobin yabo.

A nasa ɓangaren, Putin ya taya ɗaukacin jama’ar ƙasar Sin murna, bisa cikakkiyar nasarar da aka samu wajen shirya gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, da kuma yadda tawagar ƙasar Sin ta nuna bajinta. Baya ga haka, ɓangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan halin da ake ciki a ƙasar Ukraine.

Putin ya gabatar da asalin tarihin batun Ukraine, da kuma halin da ake ciki na aiwatar da matakan soji da ƙasarsa ke yi a gabashin Ukraine, da matsayin da ƙasarsa ta dauka. Ya ƙara bayyana cewa, Amurka da NATO, sun daɗe suna watsi da damuwar Rasha kan tsaron kasa yadda ya kamata, tare da yin watsi da alƙawurran da suka ɗauka, kuma suna ci gaba da tura sojoji zuwa gabas, suna kuma ƙalubalantar haƙurin Rasha. A cewarsa, Rasha a shirye take ta gudanar da shawarwari bisa babban matsayi da Ukraine.

Game da hakan, Xi Jinping ya nuna cewa, ƙasar Sin ta yanke shawara kan matsayinta ne bisa la’akari da cancantar batun Ukraine. Ya ce ya kamata a yi watsi da tunanin yakin cacar baka, da ba da muhimmanci, da mutunta halastacciyar kulawar dukkan ƙasashe a fannin tsaro, da samar da tsarin tsaron Turai mai daidaito, inganci da ɗorewa, ta hanyar yin shawarwari. Kana ƙasar Sin tana goyon bayan Rasha, da ta yi shawarwari da Ukraine don warware matsalar. Kaza lika ko da yaushe ƙasar Sin na ɗaukar matsayin mutunta mulkin kan ƙasa, da cikakken yankin ƙasa na ƙasashe daban daban, da kiyaye manufofi, da ƙa’idojin kundin tsarin mulkin MDD.

Fassarawa: Bilkisu Xin