Xi ya aike da saƙon jaje ga shugaban Afirka ta Kudu game da bala’in ambaliyar ruwa a Kwazulu-Natal

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike saƙon jaje ga takwaransa na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, don gane da bala’in ambaliyar ruwa da ta auku a yankin KwaZulu-Natal.

Cikin saƙon na sa, Xi Jinping ya ce “Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka kwashe lokaci mai tsawo ana yi a KwaZulu-Natal na Afirka ta kudu ya haifar da ambaliya, da rasuwar mutane masu yawa, kana hakan ya haifar da asarar dukiyoyi da dama”. Ya ce “A madadin gwamnati da al’ummar ƙasar Sin, da ni kai na, ina amfani da wannan dama domin gabatar da sakon ta’aziyya da jaje ga iyalan waɗanda wannan annoba ta shafa, da kuma fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.

Ya kuma yi imanin cewa, jagorancin Afirka ta kudu da kuma al’ummun ƙasar, musamman ɓangaren da wannan annoba ta shafa, za su shawo kan ƙalubalen da ake fuskanta, su kuma sake gina muhallan su cikin gaggauwa.

Mai fassarawa: Saminu daga CMG Hausa