Xi ya aike da saƙon ta’aziyya ga takwaransa na Masar kan gobarar da ta tashi a wata majami’a a Masar

Daga CMG HAUSA

Yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da saƙon ta’aziyya ga takwaransa na ƙasar Masar Abdel Fattah al Sisi, biyo bayan gobarar da ta tashi a wata majami’a a Masar.

Xi ya ce, ya firgita da samun labarin gobarar da ta tashi a wata majami’a a Masar, wadda ta yi sanadiyar asarar rayuka da dama.

Kuma a madadin gwamnati da jama’ar ƙasar Sin, da kuma shi kansa, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga wadanda lamarin ya shafa, tare da jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da wadanda suka jikkata, da kuma yiwa waɗanda suka ji rauni fatan samun sauƙi cikin hanzari.

Fassarawar Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *