Xi ya bayyana ƙwarin gwiwa game da farfaɗowar yankin Arewa maso Gabashin Ƙasar Sin

Daga CMG Hausa

Shugaban Ƙasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin ƙolin JKS Xi Jinping ya bayyana cikakken ƙwarin gwiwarsa game da farfaɗowar yankin arewa maso gabashin ƙasar Sin. Xi ya yi wannan tsokaci ne yayin rangadin sa a birnin Jinzhou na lardin Liaoning dake yankin.

Yayin ziyarar birnin a jiya Talata, shugaba Xi ya ce salon zamanantar da ƙasar Sin, na tattare da burin samar da walwala da jin dadi ga ɗaukacin al’ummar kasar ba wai wasu tsiraru kaɗai ba.

Shugaban na Sin, ya kuma yi kira da a ƙara azama wajen aiwatar da dabarun farfado da yankin na Arewa maso gabashin Sin, da ingiza tsarin raya masana’antu, ta yadda hakan zai dace da manufofin aiwatar da sauye sauye da samar da ci gaba a sabon zamani. Ya ce yana da cikakken ƙwarin gwiwa, game da farfadowar yankin arewa maso gabashin ƙasar Sin.

A yammancin jiya Talata Xi Jinping ya yi rangadin aiki a birnin Jinzhou, inda ya je ɗakin tunawa da yaƙin Liaoshen, domin waiwayen tarihin ‘yantar da yankin Arewa maso gabashin ƙasar, daga baya ya ziyarci lambun shan iska na tafkin gabas.

Yayin ziyararsa, Xi ya saurari rahotannin da aka gabatar game da yaki da ambaliyar ruwa, da kare muhallin halittu masu rai da marasa rai, inda kuma ya ba da muhimmin umurni.

Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa