Xi ya gabatar da jawabi yayin buɗe ɓangare na biyu na taron kare mabanbantan halittu na COP15

Daga CMG HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta kafar bidiyo ne ya gabatar da jawabi yayin bude bangare na 2 na taron manyan jami’ai, na kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kare mabambantan halittu ta MDD, karo na 15, da aka bude jiya a Montreal na Canada.

A cewarsa, ana bukatar cimma matsaya daya a duniya, wajen kare mabambantan halittu, da ingiza tsarin ba su kariya. Kana ana bukatar inganta kare muhalli ta hanyar kare halittun da gaggauta komawa amfani da makamashi mai tsafta a dabarun neman ci gaba da yanayin rayuwar yau da kullum, da kuma amfani da shirin raya duniya na GDI, domin moriyar al’ummun dukkan kasashe. Baya ga haka, ya ce ana bukatar daidaito da adalci wajen daukaka tsarin duniya game da kare mabanbantan halittu.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi namijin kokari wajen samun ci gaba a fannin kare muhalli da mabambantan halittu. Yana mai cewa, kasancewar halittu daban-daban da daidaito da dorewar tsarin muhallansu na ci gaba da ingantuwa.

Ya kara da cewa, kasarsa za ta mayar da hankali kan shirin MDD na farfado da halittu da muhallansu, da kaddamar da tarin muhimman shirye-shirye game da farfadowa da kare mabambantan halittu. Haka kuma kasar za ta zurfafa hadin gwiwa da musaya da kasashen waje.

Har ila yau, shugaban na Sin ya ce za su samar da tallafi da taimako ga kasashe masu tasowa ta hanyar shirin kawancen duniya na raya muhalli karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, da asusun kare mabanbantan halittu na Kunming, ta yadda za a daukaka tsarin duniya na jagorantar ayyukan kare mabambantan halittu.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *