Daga CMG HAUSA
Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmin rawar da irran ƙasar Sin ke takawa wajen tabbatar da wadatar abinci a ƙasar.
Xi Jinping ya bayyana yayin da yake rangadi a wani ɗakin gwajin tsirrai dake birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin ƙasar cewa, kiyaye albarkatun tsirrai a cikin gida, ita ce hanya ɗaya tilo ta tabbatar da wadatar abinci a ƙasar.
Ya ce domin tabbatar da albarkatun irrai sun kasance masu inganci da aminci, dole ƙasar ta kasance mai tsayawa da ƙafarta a fannin fasahar irrai.
Da yake bayyana muhimmancin ayyukan da suka shafi hakan, ya yi kira da a ɗaukaka ruhin tsoffin masana kimiyya da masu bincike, ciki har da Yuan Longping.
Ya kuma yi kira da a ci gaba da zage damtse wajen raya masanaantar irrai taƙkasar.
Mai Fassara: Faiza Mustapha