Daga CMG HAUSA
A ranar 13 ga wata, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya isar da sakon alhini ga takwaransa na Nijeriya Muhammadu Buhari, bisa abkuwar haɗarin nutsewar jirgin ruwa da ya faru a ƙasar.
Xi Jinping ya ce, ya kaɗu da samun labarin hadarin da ya auku a jihar Anambra dake ƙasar Nijeriya, wanda ya haddasa rasuwar mutane da dama.
Don haka, a madadin gwamnatin ƙasar Sin da ma jama’arta, yana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon haɗarin, tare da jajantawa iyalansu.
Mai Fassarawa: Maryam Yang