Yaƙi da cutar kwalara a Nijeriya

A cikin rahotonta na baya-bayan nan, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya ta sanar da jimillar mutane 19,228 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara, ciki har da mutuwar mutane 466 a shekarar 2022.

A ra’ayin wannan jarida, wannan lamari ne mai firgitarwa da ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin daƙile shi cikin gaggawa.

Kwalara cuta ce da ake saurin kamuwa da ita, kuma ta na haifar da gudawa da amai. Ana kamuwa da ita daga najasa ta hanyar gurɓataccen abinci, abin sha, da rashin tsafta, kuma ta na haifar da rashin ruwa a jikin ɗan adam. Yawan masu kamuwa da cutar kwalara na ƙaruwa yayin da damina ta fara. Mai cutar kwalara na iya mutuwa cikin ƙanƙanin lokaci idan har aka jinkirta ba shi kulawar gaggawa.

Ba sai an faɗa ba, dole ne gwamnati ta yi duk mai yiwuwa don kauce wa sake afkuwar cutar kwalara na shekarar 2010 da Nijeriya ta yi fama da ɓarkewar cutar kwalara a shekarun baya-bayan nan, inda aka samu rahoton mutane kusan 40,000 sun kamu, da kuma mutuwar sama da 1,500, a cewar rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya.

A shekarar 2014, Nijeriya ta samu mutane 35,996 da suka kamu da cutar sannan a shekarar 2015 an samu vullar cutar guda 2,108, yayin da 97 suka mutu. Za a iya cewa, cutar kwalara ta zama adadi mai yawan gaske a ƙasar.

Abin takaici, cutar ta Korona ta tura yawancin sauran cututtuka zuwa bango.

Cutar kwalara tana tasiri ga al’ummomin karkara da kuma marasa galihu masu ƙarancin abinci mai gina jiki, rashin ingantaccen ruwa, da rashin tsafta, don haka ba sa samun kulawar da ake buƙata daga gwamnati.

Masana sun ba da shawarar cewa yawan wanke hannu da sabulu a ƙarƙashin ruwa mai tsafta na iya hana kamuwa da cututtuka da suka haɗa da kwalara. Wannan yana da muhimmanci musamman bayan zuwa bayan gida da kuma kafin sarrafa abinci ko cin abinci.

Har ila yau, ya kamata mutane su guji yin bayan gida da kuma zubar da shara a ko ina wanda ke taimakawa wajen yaɗuwar cutar kwalara, da kuma inganta hanyoyin samun ruwa mai tsafta, tsaftar muhalli, da tsafta abinci. Wannan mataki ne mai muhimmanci don hana kamuwa da cutar kwalara da ɓarkewar cutar.

Abin baƙin ciki, Nijeriya na cikin ƙasashen duniya da ke da yawan mutanen da ke yin bahaya a fili, wanda aka kiyasta sama da mutane miliyan 46 ne. Wannan al’adar tana kawo babban haɗari ga lafiya, masu alaƙa da mutuwa daga zawo, kwalara da typhoid.

A shekarar 2016, Nijeriya ta ƙaddamar da wani shiri na kawo ƙarshen bahaya a fili nan da shekarar 2025. Shirin ya qunshi samar da ruwa da tsaftar muhalli yadda ya kamata tare da ƙarfafa hanyoyin da suka dace da al’umma wajen tsaftar muhalli baki ɗaya.

Duk da haka, matsalolin kuɗi sun ara jefa al’umma cikin haɗari. Nijeriya na buƙatar kimanin Naira biliyan 959 (dala biliyan 2.7) don kawo ƙarshen bahaya a fili nan da shekarar 2025.

Daga cikin wannan, ana sa ran gwamnati za ta samar da kusan kashi 25, wato naira biliyan 234, saboda ƙasar na yin asarar Naira biliyan 455 a duk shekara saboda rashin tsafta.

Mun kuma tuna cewa bisa ƙididdigar Bankin Duniya, Nijeriya za a buƙaci ta ruɓanya kasafin kuɗinta har sau uku ko kuma aƙalla a ware kashi 1.7 cikin 100 na Babban Kayayyakin Cikin Gida na yanzu don tsaftar muhalli.

Don haka muna kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi da su ƙara ƙaimi wajen samar da ruwa da tsaftar muhalli gwargwado iko. Ya kamata gwamnati ta kuma tabbatar da ɗorewar ayyukan ruwa a yankunan karkara.

Hakazalika, ya kamata gwamnati ta farfaɗo da yaƙin neman kawo ƙarshen bayan gida a fili a ƙasar. Har ila yau, muna kira ga gwamnati da ta qara sanya ido don ganowa da kuma sanya ido kan yaɗuwar cutar a ƙasar.

Yana da muhimmanci don inganta samun ruwa mai tsafta da wuraren tsafta. Za a iya cimma hakan ta hanyar saka hannun jari a ɓangaren samar da ababen more rayuwa, kamar gina rijiyoyi da kuma koyawa mutane ilimi da muhimmancin tsafta da wanke hannu.

Baya ga inganta samar da ruwa mai tsafta da tsaftar muhalli, yana da muhimmanci a ƙarfafa tsarin kula da lafiyar jama’a a ƙasar. Wannan yana nufin saka hannun jari ga kwararrun likitocin, da kuma samar da kayayyaki da kayan aikin da ake buƙata don tantancewa da magance cutar kwalara yadda ya kamata.

Dole ne gwamnati ta karya tsarin yadda cutar kwalara ke ci gaba da yaɗuwa a kowace shekara. Mun kuma dage cewa dole ne a sake farfaɗo da kiraye-kirayen wanke hannu a faɗin ƙasar nan.

Yadda gwamnati ta yi kira sosai kan ƙa’idojin kariya daga annobar Covid-19, ya kamata a yi irinsa kan wanke hannu a faɗin ƙasar nan, musamman a yankunan karkara.

A ƙarshe, dole ne Nijeriya ta haɗa kai da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da sauran ƙasashen duniya domin yin koyi da nasarorin da suka samu a yaƙi da cutar kwalara. Wannan zai iya haɗawa da raba mafi kyawun ayyuka don rigakafi da sarrafa carkewar cutar, da kuma haɗa kai kan bincike da ƙoƙari don nemo sabbin hanyoyin da suka fi dacewa don yaƙar cutar.

Kawo ƙarshen cutar kwalara a Nijeriya ba abu ne mai sauqi ba, amma idan aka haɗa ƙarfi-da-ƙarfe za a iya shawo kan lamarin. Ta hanyar magance tushen yaɗuwar cutar kwalara da kuma yin aiki tare da al’ummomin duniya, za mu iya kawo ƙarshen wannan mummunar cuta a ƙasarmu.

Dole ne mu yi duk mai yiwuwa don kawar da cutar kwalara a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *