Wani bincike na masana ya nuna cewa ’yan Nijeriya na cikin waɗanda suka fi fama da ciwon mantuwa a duniya.
Ciwon mantuwa da ake kira ‘dementia’ na ɗaya daga cikin cututukan da ke barazana ga lafiyar bil’adama a duniya.
Wata ƙungiyar da ta gudanar da binciken mai suna ‘Alzheimer’s Disease International’ ta ce, sama da mutum miliyan 40 ke fama da cutar a duniya ba tare da sun sani ba.
Binciken ya kiyasta cewa kashi 75 cikin 100 na ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba, kuma waɗannan alqaluma sun fi yawa a ƙasashen Nijeriya da Indiya da kashi 90 cikin 100.
Rahoton ya ƙunshi kundin nazari daga manyan masana 50 a faɗin duniya game da cutar.
Shugabar ƙungiyar, Paolo Barbarino ta ce tsangwama da rashin wayewa da rashin bincike sun taka rawa wajen samun karuwar masu ɗauke da cutar.
Hukumar Lafiya ta WHO ta kiyasta cewa adadin mutanen da ke ɗauke da cutar a duniya za su haura miliyan 130 kafin shekara ta 2050.
Binciken ya ce rashin gwajin cutar shi ne babban qalubalen da ake fuskanta, inda aka bayyana cewa ya kai kusan kashi 90 cikin 100.
Rahoton ya ce gwaji domin gano cutar na da muhimmanci, tare da ba masu ɗauke da cutar damar samun kulawar da dace da magani, wanda sun fi tasiri kafin cutar ta yi ƙarfi.
“Labaran boge daga ɓangaren lafiya, da kuma rashin samun horo a fannin ƙwararru da ƙarancin kayan aikin gwaje-gwaje, sun taka rawa wajen ƙaruwar da ake samu na gaza iya gano masu ɗauke da cutar,” a cewar Barbarino, wacce ke cikin manyan mambobi a ƙungiyar da ke taimakawa masu ɗauke da cutar ta Dementia.
Barbarino ta ce babban abin damuwarta shi ne yadda gwamnatoci har yanzu ba su shirya shawo kan hasashen da ake yi na ƙaruwar cutar a nan gaba ba. “Babu shaka, ana fuskantar tafiyar hawainiya wajen shawo kan cutar,” a cewarta.
Farfesa Serge Gauthier, kwararren likitan kwakwalwa kuma malami a Jami’ar McGill, ya ce yana dakon karvan buƙatu kan gano cutar”, yanayin da zai kasance matsi ga fanin lafiya.
A lokacin mayar da martani kan Rahoton, Richard Oakley, shugaban sashen bincike na ƙungiyar Alzheimer, ya ce gazawar gano masu ɗauke da cutar ya bar mutane cikin matsanancin hali da rashin samun goyon-bayan da suke buƙata da taimako.
Ya ce, “Ƙarancin bincike domin gano mutum na ɗauke da cutar babbar matsala ce a duniya, sai dai waɗanan alqalumma na nuna girman matsalolin. Ga waɗanda ba a yi bincike domin gano cutar ba, wannan na haifar da gajiyarwa, birkicewa da jefa su cikin yanayi na galabaita waɗanda kan kasance sakamakon yanayin da yake ciki.
“Sai dai, a yanzu binciken na da tsada, kuma ba kasafai ake samun inda ake gwajin ba, sannan har yanzu akwai tsangwama kan ambato mutum na ɗauke da ciwon mantuwa na dementia.”
Bincike ya bijiro da wani gwajin kamfuta na daƙiƙa biyu da zai iya taimakawa wajen gano ko za ka iya kamuwa da cutar nan da shekaru biyar gaba.
Wannan zai ba mutane damar soma ɗaukar matakai da shan magunguna a kan lokaci.
“Gwajin ya taimaka wajen gano mutanen da ake tunanin za su iya kamuwa da ciwon a shekarun 20 na farkon rayuwarsu, ma’ana akwai manyan damammaki da ka iya taimakawa mutum,” a cewar Dr George Stothart, na jami’ar Bath, wanda ya jagoranci binciken.
Wani sakamakon bincike da ƙasar Australia ta fitar a kwanakin baya ya nuna cewa, zama a cikin babban iyali da kula da dangantakar dangi na iya rage qaruwar matsalar cutar mantuwa.
A cikin wani bincike na ƙasa da ƙasa da aka gudanar, wata tawaga daga jami’ar Adelaide ta yi nazari kan sauye-sauye a yanayin rayuwar mutanen da suka haura shekaru 60 daga ƙasashe da yankuna fiye da 180.
Masu binciken sun gano cewa, mutanen da ke zama a cikin manyan gidaje ko suke tare da iyalai, ba su da haɗarin kamuwa ko mutuwa daga cutar mantuwa fiye da waɗanda ke zaune su kaxai ba tare da la’akari da wasu dalilai kamar shekaru da ci gaban birane ba.
Maciej Henneberg, babban marubucin sakamakon binciken ya bayyana cewa, sakamakon binciken ya tabbatar da cewa, akwai fa’idodi masu kyau ga mutanen da ke zama a cikin al’umma.
Henneberg, ya bayyana a yayin wani taron manema labaru cewa, “A cikin dubban shekaru da suka gabata, muna daya daga cikin ‘yan tsirarun da suka dogaro da zama cikin manyan gidaje, sannan kuma suka kulawa da ’ya’yansu, har sai aka samu ci gaba da wadata a cikin ƙananan al’ummomi.”
Galibi akwai lokaci da aka tsayar na cin abinci, ana yin tattaunawa, mutane su kan duba don ganin ko kun sha magungunan ku, kuma ’yan uwa suna karfafa yin aiki tare.
“Wannan haɗin gwiwa, idan ya ɗore, yana ƙara samar da sinadarin oxytocin, wanda galibi ya kan zubarar da sinadarin da ke sanya farin ciki, kuma an nuna cewa, yana da kyakkayawan tasiri a kan lafiyar jiki ta hanyar kare yanayin bugun zuciya da jijiyoyin jini da ke haxe da ciwon da ke da nasaba da jijiyoyin jini, kuma yana iya taimakawa wajen rage kamuwa da cutar mantuwa.”
A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO), fiye da mutane miliyan 55 a duniya suna fama da lalurar mantuwa, inda masu fama da cutar Alzheimer’s disease, suka kai kashi 70 cikin 100. Cutar Alzheimer’s disease, wani nau’in ciwon ƙarancin basira da da ke farawa daga matsalar mantuwa, daga bisani ya shafi tunanin mutane da ƙwarewar magana har ma da gudanar da harkokin yau da kullum. Cutar ita ce ta 7 a duniya da ke haddasa mutuwa kana an yi kiyasin cewa, an kashe kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka tiriliyan 0.8 kan cutar a duniya.
You Wenpeng, wani mai nazari a kan binciken ya bayyana cewa, sakamakon binciken zai iya yin tasiri matuƙa kan yadda ake magance cutar mantuwa.
Yana mai cewa, wannan wani muhimmin bincike ne wajen sanar da yadda muke tsara ayyukan kulawa da mutane yayin da suka tsufa, saboda yana nuna cewa, abubuwan da suka shafi ɗan Adam, da dangantaka, haɗin kai da manufa, ƙarfafawa da nuna yabo, haɗin gwiwa mai ma’ana da sauransu, duk suna da kyau da muhimmanci wajen yaƙi da cigaban lalurar mantuwa.
A ra’ayin wannan jarida, muna kira ga gwamnati a dukkan matakai da ta ɗauki matakin gaggawa wajen daƙile yaɗuwar wannan cuta a Nijeriya.