Yaƙi da korona: Gwamnati ta dawo da dokar taƙaita zirga-zirga

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin Tarayya ta dawo da dokar taƙaita zirga-zirga a faɗin ƙasa daga ƙarfe 12 na dare zuwa 4 na asuba na kowace rana a matsayin wani mataki na ci gaba da yaƙi da cutar korona.

A cewar Dr Mukhtar Mohammed wanda mamba ne a Kwamitin Shugaban Ƙasa kan yaƙi da annobar korona, wannan doka ta soma aiki ne daga tsakar daren Litinin, 10 ga Mayu, 2021.

Kazalika, Mohammed ya ce daga ranar Talata, 11, Mayu, 2021, an haramta buɗe wuraren shaƙatawa (nihgt clubs), gidajen motsa jiki da sauaransu, har sai abin da Allah Ya yi.

Ya ƙara da cewa, abin da ya shafi tarurruka na addinai, bukukuwan aure da danginsu an rage yawan mutane zuwa kashi 50, yayin da taron hukumomi an amince a ci gaba da gudanar da su ta bidiyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *