Yaƙin Badar tsakanin Buba Marwa da ’yan ƙwaya

Daga IBRAHIM SHEME

A ranar Litinin da ta gabata, sabon shugaban Hukumar Yaƙi da Safara da Shan Muggan Ƙwayoyi (NDLEA), Janar Mohammed Buba Marwa (ritaya), ya yi wata magana wadda ya kamata ta farkar da duk ɗan Nijeriya game da matsalar da fataucin muggan ƙwayoyi ke janyo wa ƙasar nan. Cewa ya yi kashi 90 cikin ɗari na muggan laifukan da ake aikatawa a Nijeriya, sakamakon ɗirkar muggan ƙwayoyi da wasun mu ke yi ne. A cewar sa, laifuka irin su hare-haren ‘yan bindiga, ta’adda, satar mutane, fyaɗe da sauran su duk ‘yan ƙwaya ne ke aikata su.

Marwa, wanda ya yi wannan maganar a tashar ruwa ta garin Onne na Jihar Ribas lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga ma’aikatan hukumar sa, ya ce: “Babu wani wanda ke cikin hayyacin sa da zai ɗauki makami ya saci mutum, ya yi fyaɗe kuma ya kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Saboda haka idan mu ka samu nasarar magance matsalar shan ƙwayoyi, to za a magance yawancin matsalolin rashin tsaro da ake fuskanta a yau.”

A wani jawabin da ya yi wa shugabannin addini a jihar kuma, Marwa ya yi gargaɗin cewa, “Idan har ba mu tashi gaba ɗayan mu mun yaƙi wannan bala’i ba a yanzu, to ya zuwa shekara ta 2050, za a samu aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 30 da ke shan ƙwaya, wanda hakan babban haɗari ne ga ɗorewar wannan babbar ƙasar tamu.”

A gaskiya, waɗannan maganganu ba abin yadawa ba ne. Janar Marwa ya yi magana wadda ya kamata ta dami kowa, domin kuwa matsalar shan muggan ƙwayoyi babba ce, musamman a tsakanin matasa. A yau, kusan babu garin da matsalar ba ta yi katutu ba, ana ta tirka-tirka da ita. Matasa da dama (wai har da mata!) sun zama ‘yan ƙwaya, wanda hakan ya na jawo matsaloli daban-daban a cikin al’ummar mu.

Matsalolin sun haɗa da na rashin tsaro kamar yadda Janar Marwa ya faɗa. To kuma akwai rashin kunya da ƙin bin iyaye ko shugabanni da yin watsi da addini da rashin maida hankali ga aiki ko sana’a da dabar siyasa da cin zarafin mata da ‘ya’ya a cikin zaman aure. Uwa-uba kuma ana samun ƙarin taɓuwar hankali. Allah kaɗai ya san illar da haɗakar waɗannan matsalolin ta ke janyo wa ƙasa ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa.

Nauyin yaƙi da ‘yan ƙwaya ya rataya ne a wuyan hukuma da ita kan ta al’umma. Shi dai Marwa, tun daga lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa shi matsayin shugaban NDLEA a farkon watan jiya na san an an aje ƙwarya a daidai gurbin ta. Dalili shi ne an daɗe ya na shugabantar wani kwamiti da Buhari ya kafa kan shawarta yadda za a kawar da amfani da ƙwayoyi ba bisa ƙa’ida ba (wato Presidential Advisory Committee for the Elimination of Drug Abuse, PACEDA) daga 2018 zuwa Disamba, 2020. Wannan aikin ya ba shi masaniya mai zurfi kan yadda ake safarar muggan ƙwayoyi da yadda ake shan su, kuma ya fahimci hanyoyin da za a bi domin a tunkari matsalar.

Da ma can Marwa ya yi kyakkyawan suna a wajen yaqi da ɓatagari a lokacin da ya riƙe muƙamin Gwamnan Jihar Legas a zamanin gwamnatin Abacha. A lokacin, laƙabin sa ma shi ne ‘Gwamna Ba-wasa’ duk da yake mutum ne mai fara’a. Akwai wani shiri da ya gudanar a Legas mai suna ‘Operation Sweep’ inda ya yi amfani da binciken sirri wajen yaƙi da ‘yan fashi da makami, ya sa su ka kwashi kashin su a hannu.

Ilai kuwa, tun da ya hau wannan sabuwar karagar, bai tsaya nawa ba, ya shiga yaƙin babu ƙaƙƙautawa. Da alama, allurar sa ta soja ba ta yi sanyi ba duk da yake yanzu shekarun sa 67 a duniya. Ya sha alwashin sai ya ga bayan manyan fataken muggan ƙwayoyi – masu shigo da su daga ƙasar waje da masu safarar su zuwa waje.

Abin burgewa, ana naɗa shi aka fara ganin canji. Marwa ya ƙwace muggan ƙwayoyi da kuɗin su ya kai naira biliyan 30 a Babban Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas. Akwai mutumin da aka same shi da kilogiram 26.840 na qwayoyi shi kaɗai, wanda an shekara sama da 15 rabon da a kama mutum guda da ɗaurin ƙwayoyi mai girman haka.

Ya aka yi haka ta faru? Saboda jami’an NDLEA sun fara sauya rawa, tunda sun ji Marwa ya sauya musu kiɗa. Sanin kowa ne cewa ana haɗa baki da wasu ɓatagari