Yaƙin Gaza: Akwai rashin adalcin majalisar Isra’ila ga ’yan gudun hijirar Falasɗinawa – Ofishin Jakadanci

Majalisar Isra’ila ta amince da dokar da ta kawo ƙarshen ayyukan MDD mai kula da ’yan gudun hijira na Falasɗinawa (UNRWA) a yankin Yammacin Kogin Jordan da Kudancin zirin Gaza, duk da rashin amincewa daga ƙasashen duniya. Wannan mataki zai kara jefa Falasɗinawa cikin ƙunci, musamman ma ‘yan gudun hijira da ke zaune a Gaza, inda kimanin yara 650,000 za su rasa damar samun ilimi. UNRWA tana ɗauke da ma’aikata 30,000 na Falasdinawa, kuma tana ba da tallafi ga kusan ‘yan gudun hijira miliyan shida, ciki har da 1,476,706 da aka yi rajista a Gaza cikin sansanoni takwas na ’yan gudun hijira, yayin da a Yammacin kogin Jordan akwai kimanin 800,000 da aka yi wa rijista.

Duk da wannan doka, matsayinsu na ’yan gudun hijira bai kamata ba saboda ana kare haƙƙin su bisa ga ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran dokokin Ƙasa da ƙasa, har sai an aiwatar da ƙudurin MDD mai lamba 194, wanda ke bai wa Falasɗinawa haƙƙin komawa ƙasarsu. Wannan mataki na Isra’ila na hana ayyukan UNRWA zai iya jefa dubban Falasɗinawa cikin mawuyacin hali, kasancewar suna dogaro da tallafin wannan hukuma wajen samun abinci, kiwon lafiya, da ilimi.

A ranar 30 ga Oktoba, daidai da kwanaki 24 na rufe yankin arewacin Gaza gaba ɗaya, al’ummar yankin sun shiga hali na ƙunci ba tare da samun agaji, kayan abinci, ruwan sha, da magunguna ba. Wannan yanayi ya janyo mutuwar mutane kusan 1000, yayin da wasu da dama suka ɓace, kuma dubban mutane sun samu raunuka daban-daban. Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa fiye da mutane 60,000 sun rasa matsugunansu a arewacin Gaza cikin watan Oktoba kadai. UNICEF ta ce yara kusan 19,000 sun rabu da iyayensu kuma suna kokarin tsira da kansu.

A yankin Yammacin kogin Jordan da birnin ƙudus, an kama mutane 11,500 ciki har da mata 430, yara 750, da ’yan jarida 132. Bugu da ƙari, an samu rahoton mutuwar fursunoni 41 waɗanda ake ci gaba da riƙe gawarsu, yayin da ofisoshin UNRWA fiye da 200 suka lalace. A Gaza kaɗai, aƙalla ma’aikatan UNRWA 232 aka kashe.

Bisa rahoton bincike da aka gudanar a Isra’ila a ranar tunawa da harin 7 ga Oktoba, kashi 6% na Isra’ilawa ne kacal suka bayyana bukatar a dakatar da yaƙin Gaza, duk da yadda yake laƙume rayuka da yawa. Wannan ya nuna yadda Isra’ila ke ci gaba da yaƙar Gaza ba tare da tausayi ga rayukan al’ummar yankin ba.

Ƙudirin da MDD ta tsara na cimma burin ci gaban duniya nan da shekarar 2030 yana ɗauke da alƙawarin cewa babu wanda zai rasa damarsa. Amma a kalaman Falasɗinawa, wannan alƙawari ba ya cika a gare su, domin suna ganin an bar su a baya, kamar yadda jakadan Falasɗinawa, Abdullah M. Abu Shawesh, ya bayyana a cikin wata sanarwa.