Yaƙi da bautar da yara ƙanana

Sanarwar da Ƙungiyar Ƙwadago ta Majalisar Ɗinkin Duniya (ILO) ta yi na baya-bayan nan ya nuna cewa, sama da yara miliyan 152 ko kusan ɗaya cikin yara 10 a duniya na fama da tilastawa wajen aure ko yin aikin ƙwadago wanda hakan ba wai kawai abin baƙin ciki ba ne amma har da nuna rashin mutuntaka.

Ƙungiyar ta ce, ƙananan yara sama da miliyan 10 ke aiki a matsayin baran gida ko kuma masu hidima a qasashen duniya, wanda ake danganta shi da bauta. Ƙididigar da hukumar ta bayar cikin makon da ya gabata, ya nuna cewa, cikin adadin kashi 3 bisa 4 daga cikinsu, ’yan mata ne, kana kuma sama da miliyan 6 da rabi daga cikin yaran, shekarun su basu wuce 5 zuwa 14 ba. Ƙungiyar ta ce, matsalar na da girma a duniya, sai dai kuma tafi qamari a ƙasashen Burkina Faso, Ghana, Cote d’Ivoire da Mali da Nijeriya. Rahotan ƙungiyar ya kuma koka kan yadda ake tura ƙananan ’yan mata daga Habasha zuwa Gabas ta tsakiya don aikin bauta a gidaje.

Ko da yake binciken na ILO da aka gudanar tare da ‘Walk Free Foundation’ ya nuna raguwar miliyan 94 a ƙididdigar da aka yi a shekarar 2000, adadin waɗannan yara masu fama da talauci, masu fama da rashin abinci mai gina jiki da kuma yawan aiki, waɗanda ba su isa su kula da kansu ba, ba ƙaramin ƙalubale ba ne a duniya.

A cewar ƙungiyar ta ILO, yara miliyan 73 ne ke yin aiki mai hatsarin gaske wanda ke katse lafiyarsu, kare lafiyarsu da kuma ci gaban ɗabi’a kai tsaye.

Jaridar Manhaja ta zaƙulo illar kai ƙananan yara aikatau don neman kuɗi, inda wannan wata matsala ce gagaruma da ta tunkaro mu a Arewacin ƙasar nan na ɗaukar yara matasa ana kai su birni gidajen masu kuɗi a matsayin masu aiki domin a biya su duk wata. Da ga cikin ayyukan da su ke yi sun haɗa da; Wanke-wanke, shara, goge-goge, yi wa yara wanka, wankin yara, wankin banɗaki, rainon yara, harma da girki.

Waɗannan ayyukan da muka lissafa wasu daga cikin ayyukan da ake sa su ne wanda yake kawo sanadiyyar gurɓacewar tarbiyyar yaran, sakamakon ba su da lokacin zuwa islamiyya ballantana boko. Sannan kuma wasu ma lokutan da za su yi sallah ba su da shi, koda yaushe suna cikin aiki. Tirƙashi, wata babbar masifa ma ita ce, bayan wahala tuƙuru da yaran kan sha sun zama su ne ma matan gida sai kuma ya zamto da zarar sun yi ba daidai ba ba a raga musu ɓalle ai musu uzuri sai duka da hantara, in ka ga gun kwanansu ma sai kai musu kuka.

Wannan babbar matsala ce, kuma ƙalubalene babba ga iyayan yarannan da kuma al’umma gaba ɗaya. Kamar yadda masu iya magana su ka ce ai ‘talauci ba hauka bane’ da iyaye za su dinga tura yaransu mata suna wulaƙanta. Ba anan gizo ke saƙar ba ma, matsalar yanzu ita ce sai ka samu maigida yana neman ɗiyar aikin matarsa ta hanyar da bata dace ba, yaran gida ma haka suma ba abarsu a baya ba wajen lalata waɗannan yara. Dubi matsalar fyaɗe ga ’ya’ya mata.

Abin baƙin ciki, ɗaya cikin biyar na waɗannan yara marasa jin daɗi ana iya samun su a Afirka, wanda ke da adadin mafi girma na kusan miliyan 72 kuma mafi girman kashi 47 na duk yaran da ke aikin tilas a duk faɗin ƙasar da duniya baki ɗaya.

Bisa ga ginshiƙi, Asiya da yankin Pasifik sun kai miliyan 62, Amurka – miliyan 11, Turai da Asiya ta tsakiya – miliyan shida, da Gabas ta Tsakiya – yara miliyan ɗaya, a nau’o’i daban-daban na tilasta ga yara.

Binciken ya kuma yi iƙirarin cewa, fiye da kashi biyu bisa uku na waɗannan yaran suna aiki ne a gonaki ko kuma kasuwancin iyali tare da kashi 71 cikin ɗari gaba ɗaya suna aikin noma.

Ƙungiyar ta kuma yi nuni da cewa, tara daga cikin 10 na waɗannan yara suna zaune ne a ƙasashen Afirka, Asiya da yankin Pacific, inda yankin kudu da hamadar Sahara ke fuskantar ƙaruwar lamarin tsakanin shekarar 2012 zuwa 2016.

Ko da yake babu wani ƙididdiga a hukumance kan yawan adadin tilas ɗin da ake yi wa ƙananan yara a Nijeriya, da sauran manyan biranen Nijeriya, da yara sama da miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta, a cewar wani ƙididdiga na Majalisar Ɗinkin Duniya na baya-bayan nan, mai yiwuwa ba a fita ba inda za a bayyana cewa ana

samun yawan yaran Afirka da ke aikin tilastawa a Nijeriya. Wannan yanayin ba shi da karɓuwa idan aka yi la’akari da yadda ƙasar ke da albarkatun ƙasa.

Jaridar Blueprint ya bayyana cewa, Nijeriya na da dukkan alƙaluman bunƙasa aikin yara, yanayin tattalin arzikin da ya yi sanadin mutuwar ‘yan kasuwa da rashin aikin yi, rikicin Boko Haram wanda ya raba mutane da gidajen kakanninsu tare da tilasta rufe gidajensu, kasuwanci da makarantu, rikicin ƙabilanci da ya shafi manoma da makiyaya da sauran bala’o’i da rikice-rikice, duk sun sanya yaran Nijeriya cikin mawuyacin hali. Ɗaruruwan sansanonin ‘yan gudun hijira na cikin gida (IDPs) sun bazu ko ina a faɗin ƙasar nan.

Mun gano tare da shawarwarin ILO na haɗin gwiwar duniya don magance yanayin aikin tilasta yin aiki ta hanyar ɗaukar ingantattun shirye-shiryen ba da taimako, na zamantakewar al’umma da sauran shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki waɗanda ke magance wasu daga cikin waɗannan ƙalubalen kai tsaye.

Kamar yadda binciken ya gani daidai, albarkatun da ake buƙata don magance matsalolin sun zarce kuɗin da gwamnatocin cikin gida daban-daban ke bayarwa.

Waɗannan munanan martanin sun sa tattara albarkatun ƙasa da ƙasa ya zama muhimmanci idan yaƙin da ake yi da aikin yara zai yi tasiri.

Duk da haka, yayin da muka yaba da ƙoƙarin da gwamnatin tarayya da na jihohi suke yi na abin sha’awa ne da kuma bunƙasa komawa makaranta ta hanyar haramta barace- barace da yara ƙanana ke yi, shirin ciyar da makaranta kyauta, aikin ci gaba na maido da zaman lafiya da kuma sauƙaƙa komawar ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu, shawo kan matsalar da ake fama da shi a yankin Neja-Delta a halin yanzu da dai sauran tsare-tsare da ke da nufin samar da yanayi mai kyau na daidaita harkokin zamantakewa da tattalin arziki, ana sa ran za a yi fiye da haka.

Rashin wutar lantarki a ƙasar wanda ya yi illa ga ƙananan sana’o’i da wanda hakan ya tilastawa da dama daga cikinsu rufe shaguna na buƙatar a gaggauta magance su. ’Yan ƙalilan da suka samu damar gudanar da ayyukansu sun durƙusar da ma’aikatansu, yayin da wasu kuma da ƙyar suke iya biyan buƙatunsu na kuɗi na wata-wata ga ma’aikatansu, lamarin da ya sanya matsin lamba ga talakawa.

Idan Nijeriya da sauran ƙasashen duniya na fatan ganin an samu ɗorewa, shirin ci gaba (SDP) na 8.7 bisa ɗari da kuma kawar da duk nau’o’in aikin yara nan da 2025 kamar yadda aka tsara, to babu makawa haɗin gwiwar duniya zai yi nasara.