Yaƙi da Boko Haram: Buhari ya kunyata Afirka – inji ɗan jairida a Ghana

Daga FATUHU MUSTAPHA

Ɗan jaridar Ƙasar Ghana, Kwesi Pratt Jr, ya ce ya ji kunya matuƙa da ya ji cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda tsohon soja ne, ya nemi ƙasar Amurka da tallafa wa Nijeriya kan batun yaƙi da matsalolin da suka addabi ƙasar.

Ɗan jaridar ya ce Shugaba Buhari ya tattara ya bar ofishinsa tun da ya gaza cika alƙawarin da ya ɗaukar wa ‘yan Nijeriya.

Shugaba Buhari yayin wata ganawa da Ƙaramin Sakataren Amurka, Anthony Blunkrn, a Talatar da ta gabata ya ce ya kamata ya yi a maida AFRICOM zuwa Afirka don ƙarfafa ƙoƙarin da ake ci gaba da yi na yaƙi matsalolin tsaro.

Yayin ganawar tasu, Buhari ya ce “Ƙalubalan tsaro su ne manyan matsalolin da suke addabar Nijeriya, kuma sun yi mummunan tasiri a sassan Afirka.

“Duk da halin da ake ciki, Nijeriya da askarawanta na ci gaba da bada himma wajen yaƙi da matsalolin daga tushensu. Sai dai akwai buƙatar neman agaji daga ƙasa kamar Amurka domin kuwa, tasirin rashin tsaron ka iya shafar dukkan ƙasashe, don haka akwai buƙatar neman haɗin kan ƙasashe domin a haɗa ƙarfi wuri guda wajen magance waɗannan matsaloli.”

Da yake jawabi a wata tashar talabijin, Mr Pratt ya nuna takaicinsa game da agajin da Shugaba Buhari ya nema duk da alwashin da ya sha yayin yaƙin neman zaɓe a 2015 na cewa zai kawar da matsalar tsaro idan ya zama shugaban ƙasa.

“Na ji kunya matuƙa da abin da Shugaban Nijeriya ya yi, Buhari ya ba ni kunya,” in ji dan jaridar a daidai lokacin da yake tsokaci kan abubuwan da Buhari ya ce zai aiwatar a lokacin da yake gudanar da yaƙin nemam zaɓe.

Haka nan ya ce, “Me Buhari ya faɗa wa ‘yan Nijeriya a lokacin da yake yaƙin neman zaɓen kwaɓe Goodluck Jonathan? Cewa ya yi shi tsohon janar ne, kuma zai iya daƙile ‘yan Boko Haram, ko ba alƙawarin da ya ɗauka ba kenan a wancan lokaci?”

“Yau shi Buharin ne kuma da kansa ke faɗa mana cewa ya gaza ba zai iya kawar da Boko Haram ba yana mai neman a shigo a tallafa mana.”

Bisa wannan dalili ne Mr Pratt ke ganin babu abin da ya kamaci Buhari face ya ajiye muƙaminsa tun da ya gaza magance matsalar tsaron da ta dabaibaye ƙasa.