Ya ɗirka wa ’yar shekara 13 da su ke haya a gidansa ciki

Ana zargin wani magidanci a Kano da ɗirka wa wata ’yar shekara 13, wadda mahaifiyarta ke zaune a gidansa ciki.

A wata tattaunawarta da manema labarai, yarinyar ta ce tun da farko mutumin ya yi mata barazanar yanka ta da kuma tashin su daga gidansa ko su biya shi kuɗin haya, matuƙar ta faɗa wa mahaifiyarta cewa yana lalata da ita.

Yarinyar ta ce yanzu haka sun je asibiti saboda cikinta ya tsufa, amma likitoci sun ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba, sai an yi mata aiki, don haka sai sun kawo jinin da za a qara mata da sauran kayayyaki, su kuma ba su da halin yin hakan.

Ta ce, mai gidan nasu yana zuwa wurinta ne idan mahaifiyarta ba ta nan, “Sai ya ce idan na faɗa mata zai yanka ni ko ya tashe mu daga haya.

“Dama kuma ba kuɗin yake karva ba, saboda da bakinsa ya ce ya ba mu kyauta, tsoron haka ya sa ban faɗa mata ba ni kuma.

“Ba zan iya tuna ranar da ya fara kwantawa da ni ba, amma dai tun kafin ranar Arfar Babbar Sallah ne,” in ji ta.

Dangane da koya na da mata a lokacin, yarinyar ta ce babu tabbas, saboda iya masu sayar da fura ta ga suna shiga gidan nasa.

Ta kuma ce ba shi kaɗai ne ya taba amfani da ita ba, domin akwai wani lokaci da har waya ya saya mata, bayan ta ba shi kanta, sai dai ya tsere.

“Ba shi kaɗai ba ne akwai wani da ya saya min waya ƙarama aka kwace da na je kai caji. Amma cikin ba nasa ba ne na wanda muke haya a gidansa ne,” in ji ta.

Haka kuma ta nemi taimakon al’umma musamman kan jini da sauran kayayyakin da likitoci suka ce sai an tanada sannan ayi mata aiki a ciro ɗan, kasancewar ba za ta iya haihuwa da kanta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *