Ya auri jikarsa kuma ya ƙi rabuwa da ita

Wani magidanci mai suna Alhaji Musa Tsafe mai shekaru 47, ya dage kan ƙin sakin jikarsa wadda ya aura shekaru 20 da suka gabata.

Mutumin wanda ke zaune a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara tare da iyalinsa, ya ce, ba zai sawwaƙe wa jikar tasa ba duk da an ankarar da shi a kan haramcin igiyar auren da aka ƙulla a tsakaninsa da ita.

Bayanai sun ce, matar mai suna Wasila Isah Tsafe mai kimanin shekaru 35, wadda jika ce ga babban yayan Alhaji Musa, ta haifa masa ’ya’ya takwas a tsawon shekaru 20 na aurensu.

Sai dai wannan lamari da ya ɗauki wani sabon salo, ya ƙara jefa rayuwar ma’auratan cikin ruɗani, inda ma’abota sani na addinin Musulunci suka sanar da Masarautar Tsafe kan haramcin auren.

Shugabannin al’umma da malaman addinin Musulunci da suka gayyaci ma’auratan domin su binciki lamarin, sun gano cewa auren ya sava wa koyarwar addini.

Hakan ce ta sanya Malaman suka shawarci Alhaji Musa a kan ya saki matarsa ​​amma ya yi biris ya ce ba za ta saɓu ba.

Wannan kuwa na zuwa ne duk da malaman sun halasta ’ya’yan da suka riga suka haifa, sai dai sun ce a yanzu da aka gano yadda lamarin ya ke, aure ya haramta a tsakaninsu.

Bayan ya ƙeƙashe ne aka miqa lamarin zuwa Hukumar Hisbah da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe, wadda kuma nan da nan aka garzaya wata Babbar Kotun Shari’ar Muslunci da a yanzu ta sanya jiya Alhamis 21 ga watan Yuli a matsayin ranar ci gaba da sauraron ƙarar.

Ana tsaka da wannan taƙaddama ce, Alhaji Musa ya garzaya wajen Sheikh Dahiru Bauchi, yana mai koken cewa wannan wata kitimurmura ce ta neman a sanya tsare-tsaren aƙidar ’yan Izala a cikin lamarin aurensa.

Sai dai Shehun Malamin wanda shi ne jagoran Ɗarikar Tijjaniya na Nijeriya, ya tabbatar da maganar malaman ta cewa auren ya haramta, sai dai shi kuwa Alhaji Musa ya ce ya ji ya gani don kuwa shi da matarsa mutu-ka-raba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *