Daga CMG HAUSA
A wajen bikin ƙaddamar da ganawar ministocin harkokin wajen ƙasashen BRICS da aka yi ta kafar bidiyo da yammacin jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi, inda ya jaddada wasu muhimman batutuwa biyu, dake haɗe da tsaro da ci gaba, ya kuma nanata cewa, a matsayinsu na ƙasashen dake bada gudummawa wajen gina duniya, ya kamata ƙasashen BRICS su tsaya haikan don fuskantar ƙalubaloli, da tabbatar da zaman karko, da samar da kuzari na raya hulɗoɗin ƙasa da ƙasa.
Tsaron siyasa muhimmin jigo ne na hadin-gwiwar ƙasashen BRICS. Tuni shugaba Xi ya gabatar da shawarar tabbatar da tsaron duniya, kuma a jawabinsa na wannan karo, shugaba Xi ya sake nanata muhimmancin shawarar, da bayyana cewa, ya dace ƙasashen BRICS su kula da muradun juna sosai, da girmama juna a fannoni daban-daban, da adawa da ra’ayin babakare ko kuma mulkin danniya, a wani ƙoƙari na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a fannin tsaro.
Bugu da kari, wani muhimmin aiki na daban dake gaban ƙasashen BRICS shi ne samar da ci gaba. Shawarar samar da ci gaba ga duk duniya da shugaba Xi ya ɓullo da ita, a watan Satumbar bara, ta samu goyon-baya daga ƙasashe sama da 100, gami da ɗimbin ƙungiyoyin ƙasa da kasa, ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya. Kuma a cikin jawabinsa a wannan karo, shugaba Xi ya ƙara da kira da a fadada haɗin-gwiwa, da inganta ƙarfin samar da ci gaba.
Duk da cewa annobar COVID-19 na ci gaba da yaɗuwa, kana kuma tsaron kasa da kasa da murmurewar tattalin arzikin duniya na fuskantar ƙarin kalubaloli, amma muddin ƙasashen BRICS sun zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, wajen kula da batutuwan da suka shafi tsaro da ci gaba, da ƙara samun fahimtar juna a fannin siyasa, da ɗaukar matakai a zahirance, babu tantama za su kara taka rawa a duk duniya, da sanya muhimmin ƙarfi ga ci gaban duniya baki ɗaya.
Fassarawa: Murtala Zhang