Ya dace a ƙarfafa gwiwar masu aikin alheri?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Masu hikimar magana na cewa, yaba kyauta tukwici. Ma’ana, idan har ka ji daɗin kyautatawar da aka yi maka, ko wani alheri da aka aiko maka to, yana da kyau ka bai wa wanda ya aikata ko ya yi sanadin sada ka da wannan alheri, wani abin tukwici ko wata kyauta da shi ma zai ji daɗi. Yabawa ko da ta fatar baki ce tana da daɗi kuma tana ƙara ƙarfafa gwiwar wanda aka yi wa, don ya sake dagewa ya yi aikin da ya dace wanda kuma zai jawo masa yabo.

Hatta a koyarwar addini ma, ana koyar da mutane muhimmancin sakanta alheri da kyautatawa. Ko a Hadisi ma an ruwaito cewa, duk wanda ba ya godewa mutane to, ba zai godewa Allah ba. Yana daga cikin wannan hikima addini yake bayyana irin ladan da Allah ubangiji ya tanadar wa bayin sa waxanda suka yi aikin alheri ko wani aiki na ibada.

Mai yiwuwa ka yi tambayar mai ya sa nake ta wannan bayani ne? Na kawo waɗannan bayanai ne domin yin shimfiɗa ga saƙon da nake son isar wa yau, da ya ƙunshi yabo da jinjina ga ayyukan alheri da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na lll yake yi, na kyautatawa da nufin ƙarfafa gwiwar Musulmi da sauran ‘yan Nijeriya da suka yi wani abin bajinta ko suka nuna wata kyakkyawar koyarwar addinin Musulunci a aikace.

A ranar Asabar da ta gabata, na shaida miƙa wani saƙon kuɗi har Naira dubu 500 da Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya aikawa wani bawan Allah mai aikin Keke Napep, ko kuma A Daidaita Sahu kamar yadda ake kira a wasu wuraren, sakamakon wani aikin alheri da ya yi, wanda ya mayar da shi abin kwatance a cikin Musulmi.

Wannan al’amari dai ya faru ne a cikin garin Jos, babban birnin Jihar Filato, inda wani bawan Allah mai suna Aƙilu Haruna Ahmad ya tsinci ɗaurin wasu kuɗaɗe, da wasu fasinjoji suka manta a cikin kekensa na aiki, lokacin da ya ɗauke su don kai su inda za su hau motar zuwa kasuwar ƙauye. Daga bisani ya gano adadin kuɗin nan sun kai rabin miliyan, bayan da ya koma inda ya ɗauki mutanen nan domin yin cigiya, sai kuwa ya tarar sun koma suna jimamin ɓatan kuɗaɗen, shi kuma ya mayar musu da ɗaurin da ya tsinta.

Labarin wannan hali nagari da tsoron Allah da Malam Aƙilu Ahmad ya nuna, duk da halin talauci da ƙuncin rayuwa da ya ce yana fuskanta, wajen kula da ɗawainiyar gidan sa, ya yi yawo a zaurukan sada zumunta, inda wasu ke ta mamaki jin cewa a Nijeriya ta yau za a samu mutum mai tsoron Allah da danne zuciyar sa irin haka. Wasu kuma har zagi suke yi da izgilanci suna cewa, ba shi da ƙashin arziki ne.

Da yake na Allah aka ce ba ya ƙarewa, kuma dama masu hikimar magana na cewa, alheri danƙo ne, ba ya faɗuwa ƙasa banza. Labarin abin da ya faru a Jos ya kai kunnen Mai Alfarma Sarkin Musulmi, inda ya sa aka yi masa binciken gaskiyar abin da ya faru, da aka tabbatar masa da hakan, shi ne ya aika wa shugaban ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam na Jihar Filato, Mai Martaba Sarkin Wase Muhammad Sambo Haruna, daidai adadin kuɗin da wannan mai aikin Keke Napep ya tsinta kuma ya mayar, domin yabawa da dauriya da kyakkyawar halayyar Musulunci da ya nuna.

Wannan ba shi ne karon farko da na shaida irin wannan halin alheri da kyautatawa da Mai Alfarma Sarkin Musulmi yake nunawa ga masu irin wannan hali nagari ba, waɗanda suka zama abin alfaharin Musulunci. Wani lokaci cikin shekarar 2019 wani mai aikin Keke Napep misalin wannan ta faru da shi, inda wata mata ‘yar ƙabilar Ibo da ke sana’ar saye da sayarwa a Babbar Kasuwar Jos ta manta da ƙunshin wasu kuɗaɗe da yawan su ya kai Naira dubu 350.

Shi kuwa yana ganin kuɗin sai ya nemi shugabannin ‘yan kasuwar ya miƙa musu kuɗin, don su yi cigiyar matar, ba a jima ba kuwa aka gano shagon da matar ke kasuwanci kuma aka mayar mata da kuɗaɗen ta, nan ma wannan labarin ya yi ta yawo a bakin ‘yan Nijeriya da kafafen sadarwa, har dai ta kai ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya sa aka nemo mutumin wanda shi ma yake aiki da keken haya da yake karva daga wajen wani yana biyan sa.

A wancan lokacin alherin da Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi har da matar mutumin da ya yi tsintuwar kuɗin, domin ya bayyana rawar da ta taka wajen ƙarfafa masa gwiwar ya mayar da kuɗin, kada su ci haram.

A wancan lokacin an saya wa mutumin sabon Keke Napep, sannan aka saya wa matarsa injin ɗin markaɗe da firji na sayar da ƙanƙara da ruwan sanyi. Duk daga saƙon Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

Wannan game da abin da ya faru a Jos kenan, ban san yawan irin waɗannan ayyuka na kyautatawa da ƙarfafa gwiwar masu aikin kare martabar Musulunci da yake yi ba a wasu jihohin Nijeriya. Musulmi da dama a wurare daban-daban suna ayyuka irin wannan na tsare gaskiya, tsoron Allah da sadaukarwa saboda Allah, ba don kwaɗayin samun wani abu ba, ko kuma don a yaba musu ba. Amma idan aka samu wani shugaba ko mai hannu da shuni da zai riƙa duba kyakkyawar niyyar mutum ya tallafa masa da wani abu a matsayin tukwici, babu shakka hakan zai yi matuƙar qarfafa gwiwar wasu su riƙa tunanin ban da sakayyar Allah akwai kuma ta duniya.

Shi aikin alheri da mutum zai aikata da kyakkyawar niyya, yana kasancewa tamkar shimfiɗa ce mutum yake yi wa kansa. Masu hikimar magana na cewa, alheri gadon barci ne. Ko ba domin wani ya sakanta maka ba, a zuciyar ka ma za ka ji natsuwa da kwanciyar hankali cewa ka yi abin da ya dace.
A lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, tsohuwar ministar sadarwa marigayiya Farfesa Dora Akunyili ta ƙaddamar da wani gangami na gyaran ɗabi’un ‘yan Nijeriya, wanda aka sanya wa suna ‘Do the right thing’. Gangamin da ke kira ga aikata abin da ya dace a kowanne lokaci. Ko da yake yanzu an jingine wannan shirin gangamin na wayar da kan ‘yan ƙasa, kamar yadda sauran shirye shirye masu kyau irin sa suka ɓace, a kwandon shara.

Ya kamata gwamnatin tarayya da na jihohi su ƙirƙiro da wani shiri da zai riƙa qarfafa gwiwar ‘yan Nijeriya su suna aikata ayyuka nagari da za su zama abin misali ga wasu. Kuma ya ƙara ɗaukaka sunan Nijeriya a idon duniya, ba kamar yadda ake yi wa ‘yan ƙasar nan mummunar shaida game da mugayen halayen da ake zargin wasun mu da aikatawa a wasu ƙasashen waje, ban da wanda muke gani yau da kullum a cikin gida.

Allah ya sa mu fi ƙarfin zuciyar mu, ya kuma ba mu ikon aikata aikin alheri, ba don ganin ido ko don riya ba.