Ya dace a hanzarta tsagaita buɗe wuta

Daga CMG HAISA

Kwamitin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya, ya kira taro kan halin da ake ciki a Ukraine a jiya Talata, inda “batun Bucha” ya zama abun da ya fi jawo hankali.

Zaunannen wakilin ƙasar Sin dake MDD ya jaddada cewa, duk wani zargin da aka yi, ya kamata ya samo asali daga haƙiƙanin gaskiya, kuma kafin a cimma sakamako, ya dace ɓangarori daban-daban su yi haƙuri da kaucewa nuna wa juna yatsa. Irin wannan ra’ayi na kasar Sin, ya samar da wata dabarar daidaita “batun Bucha” yadda ya kamata.

A halin yanzu, ɓangarorin Rasha da Ukraine suna ka-ce-na-ce kan “batun Bucha”.

Amma wasu ƙasashen yammacin duniya, ciki har da Amurka, ba su jira fitowar sakamakon bincike ba, maimakon hakan sun fara ɗaukar matakai kan Rasha. Ke nan wani al’amarin da ba’a tantance ainihin gaskiyarsa ba, ya zama hujjar da ‘yan siyasar Amurka, da na sauran ƙasashen yamma ke amfani da ita wajen sanyawa Rasha takunkumi.

Manazarta na ganin cewa, “batun Bucha” ya wakana daidai lokacin da aka cimma tudun dafawa, a yayin shawarwarin Rasha da Ukraine, kuma akwai yiwuwar ya zama makircin da aka ƙulla don kawo cikas ga shawarwarin, musamman mutanen da ba sa son ganin an kawo ƙarshen rikicin ƙasashen biyu.

Bai dace a siyasantar da batun nuna ra’ayin jin kai ba. Ƙasar Sin ba za ta amince da duk wani harin da aka kai kan fararen-hula ba, kuma bai kamata ya faru ba, ya zama dole a binciki ainihin musabbabin faruwarsa. Amma kafin a fito da sakamakon binciken, ya dace ɓangarori masu ruwa da tsaki, su kaucewa rura wutar rikici, domin mutunta fararen hula da suka rasa rayukansu, al’amarin da kuma zai hana ɓullar ƙarin matsalolin jin kai.

Fassarawa: Murtala Zhang