Ya dace Sin da Afirka su bunƙasa haɗin gwiwar cin gajiya daga fasahohin amfani da makamashi maras illa ga muhalli

Daga CMG HAUSA

Yayin da hankulan duniya ke ƙara karkata ga yadda za ta ƙarke a taron COP27, na ɓangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD, masharhanta da dama na ganin taron babbar dama ce ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki, ta su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen lalubo dabarun gaggauwa na shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi, ciki kuwa har da dabarun rage raɗaɗin sauyin yanayin, da gano fasahohin jurewa da ɗorewar rayuwa tare da ƙalubalen, da rage asarar da sauyin yanayin ka iya haifarwa, da ma batun samar da kuɗaɗen gudanar da waɗannan ayyuka.

Tuni dai aka yi imanin cewa, nahiyar Afirka na cikin yankunan duniya dake fitar da mafi ƙarancin sinadarai, da iska mai gurbata muhalli a duniya, amma a hannu guda, nahiyar na sahun gaba wajen ɗanɗana kuɗa daga mummunan tasirin sauyin yanayi.

Masharhanta na ganin duba da yadda ƙasar Sin ke kan gaba, wajen cin gajiya daga fasahohin daƙile sauyin yanayi, musamman fannin bunƙasa amfani da nauoin makamashi marasa gurbata muhalli, da waɗanda ake iya sabuntawa.

Kuma ƙasar ta jima da kasancewa abokiyar tafiya ga ƙasashen Afirka a dukkanin fannonin ci gaba, yanzu lokaci yayi da ƙasashen na Afirka za su faɗaɗa koyi daga ƙasar Sin a wannan fanni.

A cewar Frederick Mutesa, wani ƙwararre a fannin ilimin samar da ci gaba dan ƙasar Zambia, ƙasar Sin ta nunawa duniya ƙwazon ta a fili wajen bunƙasa ci gaba mai dorewa, da raya manufofi na daƙile ƙalubale da matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa.

Don haka lokaci ya yi da ƙasashen Afirka za su gaggauta yin haɗin gwiwa da Sin, ta yadda za su yi koyi, da kuma cin gajiyar ƙwarewar Sin a wannan fanni.

Ko shakka ba bu wannan shawara ce mai kyau, domin kuwa akasarin ƙasashen nahiyar Afirka na da albarkatu musamman na hasken rana, yayin da a ɗaya ɓangaren ƙasar Sin ke da ƙwarewa, da fasahohin bunƙasa samar da makamashi ta hasken rana, wanda hakan ke nuna cewa, idan har sassan biyu sun yi haɗin gwiwa, tabbas za a ci babbar gajiya daga makamashi maras gurbata muhalli.

Baya ga fannin raba fasahohi da ƙasashen Afirka, fannin samar da kuɗaɗen daƙile tasirin sauyin yanayi, shi ma muhimmin ɓangare ne da ƙasashen Afirka za su iya cin gajiya daga Sin, kasancewar dama akwai kyakkyawar dangantaka, da cuɗanya tsakanin ƙasashen Afirka da Sin ƙarƙashin dandalin FOCAC na bunkasa haɗin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kuma irin tallafi na samar da manyan ababen more rayuwa da ƙasashen Afirka ke samu daga Sin, ƙarƙashin manufofin samar da ci gaba na shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya.

Duk waɗannan dalilai, na ƙara nuna muhimmancin aza kyakkyawan mafari, na ingiza haɗin gwiwa tsakanin Sin da ƙasashen Afirka a fannin kare muhalli, da bunƙasa cin gajiya daga nauoin makamashi da ake iya sabuntawa.

Mai fassara: Saminu Alhassan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *