Ya harbe ƙaninsa yayin gwada maganin bindiga

Wani matashi ya harbe ƙaninsa mai shekaru 12 yayin gwada maganin bindiga a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara.

Wanda lamarin ya shafa dai ƙanin wani mafarauci ne da suka mallaki wani sabon maganin bindiga kuma suka yi yunƙurin tabbatar da ingancinsa.

Lamarin a cewar rahotanni ya faru ne a makon da ya gabata, inda wanda ya yi aika-aikar tuni ya arce ya bazama cikin daji bayan lamarin ya afku.

Da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Jami’in Hulɗa da Al’umma na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce, Kwamishina ’Yan sanda Paul Odama ya ba da umarnin a soma bincike a kan lamarin.

“Bayan sun ɗaura maganin bindigar a jikinsu, sai babban cikinsu ya yi amfani da bindigar mahaifinsu ta farauta ya harbi ƙaninsa.

“Sai dai an yi rashin sa’a maganin bai yi aiki ba, lamarin da ya sanya nan take ƙanin da aka harba ya shura,” a cewar Okasanmi.

Okasanmi ya shawarci iyaye da suka riƙa zuba idanu kan duk wani motsi na ’ya’yansu domin gudun faruwar mummunan tsautsayi makamancin wannan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *