Ya kai ɗan Kwankwasiyya, bai kamata ka maimaita kuskure iri ɗaya sau biyu ba!

Daga ABDULAZIZ T. BAƘO

Ya kai ɗan Kwankwasiyya, a shekarar 2019, Kwankwasiyya ta nuna maka ɗan takarar da za ka zaɓa a matakin shugaban ƙasa, da gwamna, da ‘yan majalisu, da sanatoci, amma ka ƙeƙashe ƙasa ka ce kai ina! “Cancanta,” bisa ra’ayin son zuciyarka da abinda ka ji mutanen gari suna faɗa, za ka zaɓa.

Ina ga ko ban faɗa maka ba, ka san irin tozarci da cin mutuncin da wannan ra’ayin naka na bin abinda ka kira “cancanta” ya jawo wa Kwankwasiyya, wanda in dai kai ɗan kwankwasiyyar ne na gaske, to tabbas an yi abubuwa da yawa da suka ƙona maka rai, sakamakon zavin da ka yi.

Muna ji muna gani muka ci zaɓen gwamna aka ƙwace shi ta ƙarfi da yaji. Kuma babu yadda muka iya tunda ba mu da wasu madafun iko a ƙasa. Haka kuma muna ji, muna gani aka ɗauki shekara uku da ɗoriya ana yi mana wulaƙanci son rai da ƙoƙarin rusa duk wasu alkhairai da Kwankwasiyya ta kawo wa jihar Kano a cikin waɗannan shekaru.

Kowacce irin tafiya ta siyasa ana gwada nauyinta ne gwargwadon adadin mutanen da take da su a madafun iko. Don haka, bai kamata a riƙa gina gida tare da kai ba, sannan kuma a wani ɓangare a riƙa rusa shi tare da kai ba.

Babbar shawara ta ita ce, ga waɗanda aka tsayar takara su yi ƙoƙari su gyara matsaloli da ɓaraka da ta wakana tsakaninsu da mutanen yankinsu. Su kuma mabiya, su yi haƙuri su jure a sasanta. Amma ko kaɗan yin bore ba zai amfane mu ba. Allah ya bai wa Kwankwasiyya nasara daga sama har ƙasa.

Abdulaziz T. Baƙo, mai sharhin a kan al’amuran siyasa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *