Ya kamata ɓangaren Amurka ya cika alƙawurran da shugabanta ya ɗauka

Daga CMG HAUSA

A ranar 14 ga watan Maris, agogon wurin, an ƙara ganawar manyan jami’an Sin da Amurka a Rome, babban birnin ƙasar Italiya.

Ɓangarorin biyu sun yi ganawar sahihanci, mai zurfi kuma bisa manyan tsare-tsare kan dangantakar dake tsakanin ƙasashensu, da muhimman batutuwan da suka shafi ƙasa da ƙasa, sun kuma amince da tabbatar da ra’ayin bai daya da shugabannin ƙasashen biyu suka cimma, ta yadda za a samar da yanayi mai kyau wajen maido da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka kan hanyar da ta dace, ta samun ci gaba mai inganci da kwanciyar hankali.

A yayin ganawar, ƙasar Sin ta sake bayyana matsayinta kan batutuwan da suka shafi yankunan Taiwan, da Xinjiang, Tibet, da Hong Kong da dai sauransu, inda ta nuna cewa, waɗannan batutuwa sun shafi muhimman muradun ƙasar Sin, kuma harkokin cikin gida ne na ƙasar, wadanda ba zaa taba yarda ƙasashen waje su tsoma baki a cikinsu ba. Wannan gargaɗi ne a bayyane kuma mai tsauri ga Amurka, sannan kuma wani jan layi ne da ƙasar Sin ta zana kan hulɗar dake tsakanin Sin da Amurka.

A yanzu haka, halin da ake ciki a ƙasar Ukraine, shi ne batun da ya fi ɗaukar hankalin ƙasashen duniya, haka kuma a yayin ganawar da Sin da Amurka suka yi ma, an tattauna kan wannan batu. Ƙasar Sin ta ƙuduri aniyar inganta shawarwari cikin lumana, kuma a ganinta, ya kamata ƙasashen duniya su goyi bayan shawarwarin zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ta yadda za a kai ga cimma haƙiƙanin nasara cikin sauri, don ganin an hanzarta sassauta halin da ake ciki.

A matsayinsa na wanda ya tada rikicin Ukraine, ya kamata ɓangaren Amurka ya saurari wadannan shawarwari tare da yin abubuwan da suka dace, don warware rikicin Ukraine a siyasance, maimakon yin akasin haka, ko yada labaran ƙarya don jirkita gaskiya da neman ɓata sunan ƙasar Sin.

Fassarawa: Bilkisu Xin