Daga CMG HAUSA
A jiya ne, ƙasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken “Batun Taiwan da ɗinkuwar ƙasar Sin a sabon zamani”, inda aka bayyana cewa, kamata ya yi a bar jama’ar ƙasar Sin su yanke shawara kan al’amuran ƙasarsu.
Wannan na nufin, batun Taiwan, harkokin gidan ƙasar Sin ne, wanda ya shafi babbar moriyar ƙasar, da kaunar da Sinawa suke nuna wa ƙasarsu, don haka ba su yarda da tsoma baki daga ƙasashen ƙetare ba.
Kafin fitar da takardar bayanin, shugabar majalisar wakilai ta ƙasar Amurka Nancy Pelosi, ta ziyarci yankin Taiwan na ƙasar Sin, ba tare da amincewar gwamnatin Sin ba, batun da ya lalata yanayin tsaron zirin Taiwan, da tsananta rikici tsakanin Amurka da Sin.
Dangane da wannan batu, ƙasar Sin ta fitar da wannan takardar bayani, don mayar da martani ga ziyarar da Pelosi ta kai yankin Taiwan, tare da yin cikakken bayani kan dabarun ƙasar Sin dangane da yadda za a daidaita batun Taiwan a sabon zamani, ta yadda hakan zai taimaka a kokarin tabbatar da zaman lafiya da walwala a yankin Asiya da tekun Pesific, gami da sauran wurare a duniya baki ɗaya.
A karon farko, takardar bisa tsari ta bayyana fatan sake haɗewar ɓangarori biyu na mashigin tekun Taiwan cikin lumana, a ƙarƙashin tsarin “kasa daya, tsarin mulki iri biyu”.
Wanda ya nuna irin babban ci gaban da yankin Taiwan zai iya samu, da ba da tabbaci ga moriyar mutanen yankin Taiwan, da samun kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasific, da ma sauran sassan duniya, da makamantansu.
A ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin, jama’ar ƙasar da yawansu ya kai fiye da biliyan 1.4 suna son ganin ɗinkuwar kasarsu cikin lumana, sai dai ba za su taba haƙura da yunkurin ‘yan aware na neman ɓalle yankin Taiwan daga ƙasar Sin ba.
Sinawa suna da niyya mai ƙarfi ta fuskar kare mulkin kai da cikakkun yankunan ƙasarsu, kana suna da hikima, da jajircewa da ake buƙata, wajen tabbatar da ɗinkuwar ƙasar Sin a nan gaba.
Fassarawar Bello Wang