Ya kamata a fuskanci matsalar satar ƙananan yara a Arewa

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Dr Aliyu Tilde, fitaccen marubuci kuma masanin ilimi, ɗan kishin ƙasa ya yi wani rubutu a shafinsa na Facebook inda ya ja hankalin ’yan Arewa game da matsalar satar ƙananan yara a jihohin arewacin ƙasar nan. Ya yi rubutun ne biyo bayan rahoton satar wasu yara daga Jihar Sakkwato da aka kai su Abuja sannan aka wuce da su Jos. A cewar rahoton har ma yaran sun fara zuwa coci kuma an canza musu sunaye, kamar yadda aka ce yaran sun faɗa.

A cewar Dr Aliyu Tilde, ‘Lallai Sakkwato ta zama hedikwatar satar yaran musulmi ƙanana zuwa Abuja ana raba su zuwa wasu sassan ƙasar nan. Banda yaƙi da ‘yan ta’adda ashe akwai wani yaƙin da ke cin Sakkwatawa ba su sani ba!’

Wannan rubutu da ya yi ya ja hankalina sosai, wanda ya sa na yanke shawarar yin wannan rubutu a wannan mako, domin jan hankalin ‘yan uwana ‘yan arewa, da gwamnati, da sauran masu faɗa a ji.

Domin haɗarin da ke tattare da wannan matsala ta satar yara, ba kawai a jihohin Hausawa Musulmi ba, kamar Kano da Bauchi, da Gombe da Sakkwato ba. Hatta a jihohin tsakiyar Nijeriya irinsu Filato, masu wannan aika-aika suna nan suna cin karensu babu babbaka.

Fiye da shekara biyar zuwa bakwai a yayin aikin jarida da na yi a Jos na ga irin mutanen da jami’an tsaro suka kama wasu mutane da ake zargi da hannu wajen satar ƙananan yara, waɗanda ma ba yaran musulmi ba. Na kawo wannan ne don mu fahimci cewa wannan matsala ba kawai tana shafar musulmi ba ne, har ma da sauran ’yan Nijeriya.

Kar ku manta a Jos ne aka taɓa kama gida na musamman da ake ajiye mata ana yi musu ciki, idan sun haihu sai a ɗauke jariran a biya su kuɗi, daga Naira dubu 350 zuwa dubu 400. Daga nan kuma sai a kai jariran Abuja ko Legas da wasu jihohin kudancin ƙasar nan, a sayar da su kan kuɗi Naira dubu 700 zuwa miliyan ɗaya.

Duk da kasancewar akwai inda matsalar addini take taka rawa, musamman abin da ya shafi yaran almajirai, waɗanda ake kwashe su a kan titi da sunan za a taimaka musu da abinci ko magani da wajen kwana, amma a ƙarshe a kai su wani waje a ɓoye su har ana ƙoƙarin canza musu suna da addini. Kamar abin da ya faru a Jos, cikin watan Yuni na shekarar da ta gabata, inda aka zargi wata ƙungiyar Kirista da satar wasu yaran almajirai daga Jihar Gombe.

Wani rahoto da jaridar Turanci ta Daily Trust ta fitar ya nuna cewa, a lokacin da jami’an tsaro na farin kaya wato DSS, suka far wa gidan bayan binciken sirri da suka gudanar sun gano yara 21 da aka kai wani gida da ke yankin Tudun Wada a garin Jos, daga cikinsu akwai yaran almajirai da waɗanda suka fito daga wasu wurare, waɗanda suka ce da qarfin tuwo aka kai su gidan, kuma ba a barinsu su fita.

Rahotanni irin wannan suna da yawa, ko da su ma yaran da aka sace su daga Jihar Kano, kuma aka gano su bayan wasu shekaru a jihohin kudu, an gano an canza musu sunaye da addini. Irin waɗannan yara da ake kai wa Kudu, an ce ana sayar da su ne ga iyalin da basu taɓa haihuwa ba, waɗanda suke a shirye don biyan maƙudan kuɗaɗe, domin su mallaki yaran. A maimakon su bi hanyar da ta dace bisa tanadin doka. Don haka suka fi son jarirai ko ƙananan yaran da ba su yi wayo ba, waɗanda ba za su iya tuna komai na rayuwarsu ta baya ba.

Dokar Kare Haƙƙoƙin Yara ta Nijeriya ta 2003 a sashi na 50 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, ta shimfixa wasu sharuɗɗan ga duk wani mai neman ɗaukar raino ko riƙon yaro daga wajen iyayensa ko daga wata hukuma ta gwamnati, ko wata ƙungiya masu kula da marayu. Akwai ƙa’idoji na wanda zai ɗauki riƙon da kuma shi kansa wanda za a ɗauka, da sauran sharuɗɗan da doka ta tanada.

Kamar yadda za a iya gani a sashi na 129 na wannan doka, wacce ta tanadi cewa, ma’auratan da suka kai shekara 25 za su iya karvar riƙon, a matsayin iyali. Ko kuma wanda ba shi da aure, amma ya kai shekaru 35, matuqar wanda za a karvi riƙon nasa jinsin su ɗaya da wanda zai karva. Abin da hakan ke nufi kuwa shi ne, namiji ba zai karɓi riqon mace ba, haka ma mace ba za ta karɓi riƙon namiji ba.

Sannan harwayau, sakin layi na (a) (b) da (c) na wannan doka da ta ba da damar ɗaukar damar riƙo ko raino an buƙaci a samu aƙalla shekaru 21 a tsakanin wanda zai ɗauki riƙon da wanda za a ɗauka, kuma lallai ne wanda zai ɗauki riƙon ya zama ya kai aƙalla shekara 25 da haihuwa.

Sannan a dokar Nijeriya masu zaman dadiro ko masu auren jinsi ba su da haƙƙin ɗaukar raino ko riƙo. Akwai kuma wasu abubuwa da ake dubawa da suka shafi halaye nagari da aikin yi ko ƙarfin riƙon, wanda ya haɗa da ƙarfin ciyarwa, tufatarwa, kula da ilimi da tarbiyya, kamar yadda yake akan kowaɗanne iyaye.

Waɗannan dokoki da wasun su da ban ambata ba su ne suke hana mutane zuwa karɓar ɗan riƙo a hukumance, sun gwammaci su bi ta ɓarauniyar hanya su sayi yaran a hannun ɓarayi da ke gudanar da harkar satar yara daga wata jiha zuwa wata. Abin da yake da doka mai tsanani a kansa.

A cewar Barista Mariya Muhammad Shittu, wata lauya mai kare haƙƙoƙin mata da ƙananan yara, idan har aka tabbatar da laifin mutum ya sace ko ya sayar da wanda ya saya akwai hukunci mai tsanani da dokar Penal Code ta tanada, wanda ya kama har da ɗaurin rai da rai.

Amma a ƙarƙashin sabuwar Dokar Kare Haƙƙoƙin Wanda Aka Zalunta ta Violence Against Persons Prohibition Law, an tanadi tara da ɗaurin shekara 17 zuwa 21, ga duk wanda aka kama da hannu a satar yaro ko saya daga iyayen yaro ko wani daban.

Wajibi ne a yabawa Majalisar Masarautar Kano ƙarƙashin Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda ya yi gargaɗi mai kama da jan kunne ga shugabannin al’ummar Igbo mazauna Jihar Kano sakamakon abubuwan da suke faruwa na satar qananan yara a jihar, biyo bayan bankaɗo gungun wasu vatagari ’yan ƙabilar Igbo da ke satar yaran da rubdunar ’yan sanda ta yi.

Lallai yana da kyau jami’an tsaro su ƙara zage damtse wajen binciken irin waɗannan gungun varayin yara da suke jefa zukatan iyaye cikin firgici da damuwa, musamman jami’an tsaro da ke aikin binciken ababen hawa a kan manyan hanyoyin ƙasar nan, waɗanda ta gabansu ake wucewa da yaran nan. Sannan su ma iyaye su ƙara sa ido da lura kan inda yaransu ke fita ko aika.

A daina barin yaran da ba su yi wayo sosai ba, suna fita cikin anguwa barkatai babu wani babba da ke sa ido a kansu. Haka kuma malamai da shugabannin makarantun rainon yara, su riƙa samar da dokoki masu tsauri game shiga da fitar yara a makaranta, musamman waɗanda suke zuwa ɗaukarsu bayan an tashi. Bayanai na nuna cewa, yawanci yaran da ake sacewa ana ɗauke su ne daga makaranta ko wajen aika.

Lallai jihohin Arewa su tashi tsaye su yaqi wannan halayya ta satar yara da take neman zama alaƙaƙai a garuruwanmu. A daina sakewa da baqi da ba a san daga ina suke ba, ko ba a yarda da ingancin halayyarsu ba, suna kusantar yaranmu, har wani lokaci su cutar da su ko su ɗauke su zuwa wani waje, sakamakon sakacinmu ko rashin kula da muke wa yaranmu.

Kullum muna gadara da yawanmu ko cewa addini ya kwaɗaitar da mu mu hayayyafa, don manzon Allah (SAWA) ya yi alfahari da yawanmu, amma kuma ba mu san yadda za mu bai wa yaran kulawa da tarbiyyar da ta kamata ba, mun bar su a titi suna watangaririya, har waɗanda suka fi mu so sun zo suna ɗauke su, suna canza musu addini.