Ya kamata a riƙa ɗaure shugabanni da suka ci rashawa – Obi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Dan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi ya ce kamata ya yi duk shugabanni da aka samu da cin hanci a Nijeriya su riƙa fuskantar tsassaurar hukunci.

Obi ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata domin bikin ranar yaƙi da cin hanci ta duniya.

A cewarsa, cin hanci ya dabaibaye dukkan matakan gwamnati a Nijeriya a tsawon shekaru.

Ya ce ƙasar na fuskantar tarin bashi da ya yi mata katutu, wanda ya faru sakamakon ciyo bashi da gwamnatoci ke ci gaba da yi.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya shawarci shugabannin Nijeriya da su zama masu gaskiya da kuma kauce wa cin hanci da rashawa.

“Kasancewar Nijeriya a jeri na 145 cikin ƙasashe 180 da aka fi cin hanci, ya nuna yadda rashawa ta yi wa Nijeriya katutu. Ya kamata a yaƙi hakan idan ana son ci gaba,” in ji Obi.

Ya ƙara da cewa Nijeriya na cikin ƙasashen Afrika 11 da ke fama da rashin kyawun shugabanci a cikin shekara 10 da suka wuce.

Ya ce hakan ya ci gaba da janyo cikas wajen samun cigaba a ƙasar.