Ya kamata a tabbatar da haƙƙin ɗan Adam cikin rayuwar jama’a

Daga BELLO WANG

A kwanan baya, muƙaddashiyar babbar kwamishina mai kula da haƙƙin ɗan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya, Nada Al-Nashif ta bayyana a cikin wani jawabinta cewa, hauhawar farashin kayayyaki na haifar da barazana ga haƙƙin raya kai na jama’ar ƙasashe masu tasowa.

A cewarta, yayin da asusun ba da lamunin duniya IMF ke hasashen ganin matsakaiciyar hauhawar farashin kayayyaki ta kashi 6.6% a ƙasashe masu sukuni a shekarar da muke ciki, hauhawar da ake sa ran ganinta a ƙasashe masu tasowa za ta iya kaiwa kashi 9.5%, bisa wani matsakaicin matsayi.

Batun nan bai ba ni mamaki ba, ganin yadda tun tuni ƙasar Amurka ke sanya bankunan ƙasar ba da ƙarin ruwan kuɗin ajiya, don neman daidaita matsalar hauhawar farashin kaya a cikin gidanta.

Sai dai matakin ya zama karkata matsin lamba da take fuskanta zuwa ga sauran ƙasashe, musamman ma ƙasashe marasa ƙarfin tattalin arziki, waɗanda suka fi jin radadin manufar.

A sakamakon haka, zuwa yanzu, darajar kuɗin Rand na ƙasar Afirka ta Kudu ta ragu da kashi 9.4%, yayin da darajar Pound na ƙasar Masar ta sauka da kashi 18%.

A ƙasar Ghana ma, ko da yake ta riga ta daga ruwan kuɗin ajiya zuwa kashi 22% don tinkarar matakin ƙasar Amurka, amma duk da haka, darajar kuɗin ƙasar na ci gaba da raguwa.

Kar mu manta da yadda ƙasar Amurka ke bayyana kanta a matsayin mai kare haƙƙin ɗan Adam a duniya.

Amma ga shi yanzu tana kwatan moriya a ƙasashe marasa ƙarfin tattalin arziki, tare da keta haƙƙin jama’ar ƙasashen na rayuwa da neman raya kansu.

Ta wannan misali za mu iya ganin cewa, “kare haƙƙin ɗan Adam” da ƙasar Amurka take yi aikin fatar baki ne kawai, wanda sam ba zai haifar da moriya ga mutanen duniya ba.

Sai dai a nata ɓangaren, yadda ƙasar Sin take fahimtar matakin “mai dokar barci ya ɓuge da gyangyaɗi” da ƙasar Amurka ke ɗauka a fannin kare haƙƙin ɗan Adam, ya sa ƙasar ke kira ga ƙasashe daban daban don su dora ƙarin muhimmanci kan kare haƙƙin ɗan Adam na raya kai da neman ci gaba.

A gun taron kwamitin haƙƙin ɗan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya dake gudana, wakilin Sin Chen Xu ya ce, ci gaban tattalin arziki shi ne tushen hakkin ɗan Adam.

A cewarsa, ya kamata ƙasashe daban daban su yi ƙoƙarin tabbatar wa al’ummunsu hakki na gaske, kuma mai amfani.

Shin mene ne haƙƙin ɗan Adam na gaske kuma mai amfani?

Na tuna da wani saurayi mai aikin jigilar kaya da na gamu da shi a nan birnin Beijing a kwanan baya.

Ya ce, ko da yake aikin da yake yi na kai abincin da aka saya ta yanar gizo ta Internet zuwa gidajen mutanen da suka sayi abincin na da wahala, amma yana samun Yuan 7 (kwatankwacin dalar Amurka 1) bisa duk wani ƙunshi da ya kai.

Yakan iya kai ƙunshi fiye da 100 a kowace rana, ta yadda yake samun fiye da Yuan 700 (fiye da dala 100) a duk rana.

Hakan zai tabbatar da albashinsa na kowane wata da ya kai fiye da Yuan 15000 (dala 2122).

To, waɗannan adadi su ne shaidar haƙƙin ɗan Adam na gaske.

Ban da wannan kuma na tuna da wani ƙauye mai suna “Xiao Hei Fa” da na kai ziyara a kwanan baya, inda na ga gwamnati na ba da tallafi ga wasu kamfanoni, domin su samar da guraben aikin yi ga mutane masu fama da lalurar nakasa.

Ta wannan hanya waɗannan nakasassu sun samu kuɗin shigar da ya kai fiye da Yuan dubu 25 (dalar Amurka 3540) a duk shekara, abun da ya sa suke iya dogaro da kansu.

Wannan irin manufar taimakawa nakasassu ita ce abin da ake kira manufar kare haƙƙin ɗan Adam mai amfani.

Haƙƙin ɗan Adam bai tsaya ga kalmomi kawai ba, ya kamata a yi ƙoƙarin tabbatar da shi a cikin rayuwar jama’a.

Ta hanyar tantance yanayin rayuwar jama’a, za a san ainihin yanayin haƙƙin ɗan Adam na wata ƙasa.

Mai fassara: Bello Wang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *