Ya kamata Amurka da wasu ƙasashen Yamma su kalli laifinsu na nuna wariya ga ‘yan asalin ƙasashensu

Daga MINA

Abokai, tun kafuwar ƙasar Amurka a ƙarni na 18, Indiyawan daji ‘yan asalin Amurka suka fara shan wahala.

Yau “Duniya a zanen MINA” zai yi bayani ne kan mawuyacin halin da suke ciki yanzu.

Tun lokacin da Christopher Columbus ya gano nahiyar Amurka, Indiyawan daji ‘yan asalin wurin suke fama da ƙalubaloli da dama.

Tun daga ƙarni na 15 zuwa na 20, fararen fata suka yi ta yiwa Indiyawan dajin kisan gilla ba tare da tsayawa ba, har suka raba yaransu da iyalansu, inda ake cin zarafinsu da hana su koyon al’adunsu, lamarin da ya kai ga ɓacewar al’adun nasu.

Har zuwa ƙarni na 21 da muke ciki a halin yanzu, Indiyawan daji suna fuskantar mawuyancin hali, Amurka da kuma Canada suna kara nuna musu wariya.

Amma, waɗannan masu aikata laifin suna zargin sauran ƙasashe da take haƙƙin ƙananan ƙabilu.

Kwanan baya, Amurka da wasu ‘yan tsirarrun ƙasashe da wakilan ƙasashen EU sun zargi ƙasar Sin game da cin zarafin ƙananan ƙabilu, zargin ba shi da tushe ko kaɗan.

Kamar yadda bayanai suka nuna, ƙabilu 56 ke zaman rayuwa cikin jituwa a yankin Xinjiang. Ana samun bunƙasuwar tattalin arzik da kyautatuwar zaman rayuwa da ci gaban al’adu da bin addinai yadda ya kamata a yankin, wannan shi ne abin da jakadun ƙasashen Larabawa da Afrika da dama dake nan ƙasar Sin suka amince da shi, sakamakon yadda suka ganewa idanunsu abubuwan dake wakana a yankin.

Abin da ya kamata Amurka da Canada da wasu ƙasashe su yi shi ne, su duba laifin da suka aikata na kisan gilla ga Indiyawan daji ‘yan asalin wurarensu, da daina nuna bambancin launin fata ga ƙananan ƙabilu ciki har da ‘yan asalin Asiya, tare da kawar da rashin adalci a cikin al’lumma, ta yadda ƙananan ƙabilu za su samu ‘yanci da bunƙasuwa cikin adalci.

Mai zane da rubuta: MINA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *