Ya kamata Gwamnati ta ƙarfafa tsaron ƙasa da karin jami’ai – Tambuwal

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da ƙarin jami’an tsaro domin tallafawa wajen ƙarfafa lamarin tsaro a faɗin ƙasar nan.

Tambuwal ya bayar da shawarar haka ne jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri’arsa a rumfa mai lamba 33 dake Makarantar Sakandirin garin Tambuwal.

A cewarsa, samar da ƙarin jami’an tsaron ba makawa zai taimaka wajen kare martabar ƙasar a idon duniya.

Game da zaɓen gwamnoni da na majalisar jihohi kuwa, Tambuwal ya buƙaci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, da ta ƙara yin shiri na musamman domin gudanar da zaɓe karɓaɓɓe.