Ya kamata gwamnati ta dinga sa mata wakilci domin samun hanyar tallafa wa mata

Hajiya Zainab Sani Giwa mace ce ‘yar gwagwarmaya kuma mai son cigaban mata ‘yan’uwan ta ta fuskar wayewa da zamantakewa da kuma samun abin dogaro da kai. Ta yi fice sosai musamman a Ƙaramar Hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna saboda kasancewar ta shugabar mata a yankin. A tattaunawar ta da jaridar Manhaja, masu karatu za su ji irin faxi-tashin da ta ke yi wajen faranta ran mata da marasa galihu.

Daga AISHA ASAS a Abuja

Masu karatu za su so jin cikakken suna da tarihin ki a taƙaice.
Assalamu alaikum. To alhamdu lillahi, suna na Zainab Sani Giwa. Ni haifaffiyar cikin Giwa ce ta Jihar Kaduna. Na yi makarantar firamare ɗi na a Giwa, sannan na zo na yi JSS 1 zuwa 3 a sakandaren gwamnati da ke Giwa, wanda a lokacin mu ne farkon ɗiba daga 1990 – 1993. Sannan na je na yi babbar sakandare a makarantar kwana ta ’yan mata da ke Soba.
Bayan nan na je Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna da ke Zariya, inda na yi IJMB, a 1996 – 1997. Na zama shugabar mata Musulmai na duka makarantar, wato ‘Annex’ da UPE, daga nan na koma FCE Zariya a 1998 – 2001 inda na karanta ‘Biology/Chemistry’.
Na samu aikin koyarwa a ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Giwa a 2002, amma yanzu haka ina cigaba da karatu na a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ina da aure da yara biyar; huɗu mata, ɗaya namiji.
Na yi aiki da ƙungiyoyi masu zaman kan su a fannin lafiya, kamar WHO, UNICEF, NURHI, da CHAI. A yanzu haka ina aiki da ƙungiyar ‘Global Initiative for Women and Children’ (GIWAC), wanda ni ce ko’odineta ta Giwa. Sannan ni ce shugabar FOMWAN ta ƙananan hukumomi guda biyar: Giwa, Birnin Gwari, Ikara, Kudan da kuma Maqarfi.

Mene ne matsayin ki a wajen matan ƙaramar Hukumar Giwa?
A yanzu ni ce shugabar ƙungiyar ‘Women Initiative Forum Giwa’, wato ƙungiyar matan Ƙaramar Hukumar Giwa, wadda ta ƙunshi Fulani, Kiristoci, naqasassu, mata matasa, da sauran su. Kuma duk ƙungiyoyin Giwa gaba ɗaya mu ka cure wuri guda mu ka samar da wannan, don ya zamana dai matan Ƙaramar Hukumar su na magana da murya ɗaya.

Mene ne aikace-aikacen ƙungiyar ku a matsayin ki na shugabar tafiyar?
To, aikace-aikacen mu shi ne taimakon juna a duk lokacin da ya taso, da koya wa mata sana’o’i kamar saqa, ɗinki, yin ɗankunne da sarƙa, da irin su gumin shinkafa ta zama kamar ‘yar ƙasar waje, saboda gwamnatin Jihar Kaduna kwanakin baya ta horas da mu yadda ake yi, kuma an ba mu kayayyakin gumin wanda su ka haɗa da tukunya da tanfol da injin ɗinke buhu, da dai sauran kayayyakin aikin.
Sannan ƙungiyar mu mu na koya wa ‘yan mata sarrafa na’urar kwamfuta, mun yi kamfe a kan annobar ‘Covid-19’, mun yi fastoci na wayar da kai da yadda za a kiyaye kai daga kamuwa da cutar mun rarraba wa mata gida-gida, kuma mun wayar musu da kai. Bayan haka nan, mun sha wayar wa mata da kai a kan cutar foliyo da shayar da yara nonon uwa zalla na tsawon watanni shida, da kuma wayar da kai a kan masu matsalar yoyon fitsari, da sauran su.
Saboda haka duk waɗannan sana’o’i da mu ka koya wa matan mun yi ne da nufin su iya dogaro da kan su ba tare da sun yi dogaro da miji ba, har ma su taimaki mijin nasu da ‘ya’yan su da sauran ‘yan’uwa.

Shin aikace-aikacen ƙungiyar taku iya Giwa ta tsaya ko kuwa har da wasu ƙananan hukumomin?
E, gaskiya ƙungiyar mu ta Ƙaramar Hukumar Giwa ce, ba tare da sako ‘yan wasu ƙananan hukumomi ba ko jiha ba. Mu na gudanar da aikace-aikacen mu cikin gundumomi 11 da mu ke da su a Ƙaramar Hukumar Giwa. Sai dai abin sha’awar, wasu ƙananan hukumomin su kan kwaikwayi irin abubuwan da mu ke yi na wayar da kan mata da tallafa masu. Kin ga ko kamfe da mu ka yi na cutar korona ɗin nan mu ka rarraba fosta da takardun mannawa a motoci ko babura, sai da wasu su ka kwaikwaye mu.

Wane ƙoƙari ƙungiyar ku ke yi wajen ganin kun wayar da kan mata musamman ta fuskar sana’o’in dogaro da kai ba dogaro da miji ba?
Na yi ƙoƙarin nema wa mata bashin kuɗi domin su ja jari. Har sun gama biyan kuɗaɗen da ake bin su, wanda wasun su sun samu hanyoyin dogaro da kan su a yanzu haka.

Wane kallo ki ke yi wa macen da ba ta da sana’a, musamman wadda ta ke ɗakin mijin ta?
Kallon da na ke wa macen da ba ta sana’a shi ne ballagaza, wacce ba ta san ciwon kan ta ba. Domin wata rana naira goma za ta iya gagarar ta, matan garin su ko unguwar su kowa sai ya raina ta, ko bashi ba mai iya ba ta don an san cewa ba ta da hanyar da za ta iya biya.

Shin gwamnati ko wata cibiya ko ɗaiɗaikun mutane su na tallafa maku wajen ganin kun bunƙasa hanyoyin tafiyar da ƙungiyar ku?
Gwamnatin Jihar Kaduna ta koya wa ƙungiyar mu gumin shinkafa domin dogaro da kai. Haka kuma Ƙaramar Hukumar Giwa duk abin da za ta yi ta kan saka ƙungiyoyin mu. Misali, an saka mace ɗaya-ɗaya daga kowace gunduma a cikin kwamitin rabon tallafin kayan rage raɗaɗin zaman gida da annobar korona ta haddasa. Kuma kowace gunduma sun fitar da marasa galihu daga cikin ƙungiyar an ba su tallafin. Sannan kuma ’yan majalisun mu dukkan su su na tallafa mana; kamar ɗan Majalisar Tarayya Shehu Baƙauye da sauran na jiha duk sun ba mu gudunmuwa wajen tafiyar da aikace-aikacen mu.

Daga dukkan alamu dai Hajiya Zainab ta na taɓa siyasa. Ko ya abin ya ke?
E, gaskiya mu na ɗan taɓa siyasa, domin na tava yunƙurin fitowa takarar shugabar Ƙaramar Hukumar Giwa, amma saboda wasu dalilai sai na fasa. Bayan haka kuma ƙungiyar mu ta na mara wa wani ɗan siyasa baya amma idan ya cika dukkan sharuɗɗa da muradun ƙungiyar mu da na mafi akasarin al’ummar mazaɓar sa.

Ki na da kiran da za ki yi wa gwamnati wajen ganin ta tallafa wa ƙungiyoyi, musamman irin naku na matan da ke neman sana’ar dogaro da kai?
Ina kira ga gwamnati da su riƙa sa mata wakilci domin su riƙa bada shawara yadda za a riƙa taimaka wa mata su dogara da kan su ta hanyar koya masu sana’o’i, a ba su jari ko abin yin sana’ar.

Mata da yawa ba sa son maigida ya yi masu maganar kishiya. Ko ke ma ki na cikin irin waɗannan matan?
Malama Asas, ki sani fa ba wai kishiya ce ba a so ba, wani mijin da zarar ya qara aure ke da banza ɗaya za ku koma, wata kuma burin ta ta kore ki, ta raba ki da mijin da yaran ki. Amma idan miji zai zamo mai adalci, ban ga wata matsala ba. Kuma faɗar Allah (SWT) da ya ce, “Ku yi aure bibbiyu, uku-uku ko huɗu; amma idan ba za ku yi adalci ba ku tsaya a guda ɗaya.”
Saboda haka ina kira ga ’yan’uwa na mata da mu yi haquri kar mu riqa tada hankalin mu don miji zai qara aure; mu yi ta addu’a, ita ce kawai mafita a gare mu, kuma mu yi fatan alheri.

Ke kaɗai ce a wajen maigidan ki ko kuwa akwai abokiyar zama?
A’a, ni kaɗai ce a wajen maigida na.

Ya za ki yi idan ya ce zai ƙara aure?
(Dariya) Ya zan yi kuwa? Zan yi haƙuri in bar wa Allah komai, ya kawo abokiyar zama tagari.

Waɗanne nasarori ki ka samu a rayuwar ki, musamman a harkar da ta shafi ƙungiya?
Kai! Gaskiya na samu ɗimbin nasarori masu yawa, saboda abin da na daɗe ina fata kenan a rayuwa ta, in ga na faranta wa maraya rai, to alhamdu lillahi na sa marayu cikin farin ciki, domin duk lokacin da na ba su kaya su kan kasance cikin jin daɗi. Sannan na taimaka wa mata da yawa sun samu abin yi, musamman matan da na sama masu aikin rigakafin VCM (’yan lafiya jari) da su ke aiki da UNICEF, wanda ni ce silar samun aikin nasu kuma duk wata su na amsar wani abu. Sannan koya wa mata sana’o’i da na yi domin su yi dogaro da kan su, da kuma taimaka wa duk wanda ya zo neman taimako ko da ba yawa, maza da mata, duk mu kan yi ƙoƙari wajen wannan. Saboda haka ina ɗaukar wannan cikin irin nasarorin da na samu a rayuwa ta. Kuma na gode wa Allah.

Ƙalubale fa, akwai su?
E, na samu ƙalubale masu yawa a rayuwa, domin duk san da zan jawo wata mace domin cigaban ta sai ta ci amana ta. Na samu irin wannan jarrabawar da yawa. Amma na kan bar wa Allah, ya na kuma kawo min mafita. Ko sun yi makircin su na ɗan wani lokaci ne, sai ki ga gaskiya ta yi halin ta, domin Hausawa na cewa a daɗe ana yi sai gaskiya, kuma ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi.

Me ya fi ba ki mamaki a rayuwar ki?
Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne yadda na ɗauko wata yarinya bayan an kori uwar ta daga aiki, na sa ta a aiki, daga ƙarshe yarinyar sai da ta yi sanadiyyar barin nawa aikin. Ga ɓatanci da ta yi min, wanda na san Allah ba zai bar ta ba, domin ni alkhairi na yi mata tsakani na da Allah, amma ta saka min da sharri. Haka rayuwa ta ke!

Wane kalar abinci ki ka fi so?
Abincin da na fi so shi ne shinkafa da miya da nama.

Wane kaya ki ka fi sha’awar sawa?
Gaskiya ni na fi sha’awar zani da riga da hijabi.

Me ke saurin sa ki fushi ko ɓata miki rai?
Abin da ke sa ni saurin fushi shi ne abin da ban yi ba a ce na yi.

Me ya fi burge ki?
Abin da ya fi burge ni shi ne in ga ina taimakon mata da abubuwan da zai kawo masu cigaba.

To mun gode, Hajiya Zainab.
Ni ma na gode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *