Ya kamata gwamnati ta fito da tsarin da zai hana matan Fulani kiwo – Ramatu Muhammed

Mafi yawan mata masu yoyon fitsari Fulani ne” – Ramatu

Daga UMAR AKILU MAJERI, a Dutse

Hajiya Ramatu Muhammed tsohuwar malamar makaranta ce. Ta kasance bafilatana mai kishin yarenta, tare da son taimakon marasa galihu. Hajiya Ramatu na ɗaya daga cikin malamai da ake alfahari dasu a cikin makarantun ‘ya’ya Mata da suke taimaka wa wajan baiwa ɗalibai tarbiyar da ake alfahari dasu a Jahar Jigawa. Yanzu haka malama Ramatu itace babbar sakatariya mai cikakken iko a Hukumar Raya ilimin ‘yayan Fulani makiyaya a ma’aikatar ilimi ta Jahar Jigawa ,kafin takai ga wannan matsayin, ta tava riƙe muƙamin daraktan makarantun ‘ya’yan makiyaya a Hukumar ilimin ta ‘ya’yan makiyayan. Wakilinmu na Jahar Jigawa ya samu damar zantawa da ita, kuma tayi bayanai masu yawa, ciki har da al’amarin da ya shafi yadda Fulani su ke rayuwa da dabbobinsu a daji da kuma dalilan da yasa mazauna Ƙasar Sudan suke shan shayi a matsayin abinci. A hirar da su ka yi, ta fara da gabatar da kanta, bayan da wakilin namu ya buƙaci hakan, inda ta fara da cewa:

RAMATU: Sunana Hajiya Ramatu Muhammed, ni ce shugaban Hukumar Raya ilimin ‘ya’yan Fulani makiyaya ta Jahar Jigawa.

MANHAJA: A matsayin ki ta mace kuma bafilatana, wane irin ƙalubale ki ka fuskanta a wajan abokan aiki?

Ni ba wani ƙalubale da na fuskanta a rayuwata ta aikin gwamnati, kasancewar Allah ya tsareni, kuma na kama kaina. Ƙalubale da na samu bai wuce na ƙoƙarin baiwa yara tarbiya ba. A lokacin da nake koyarwa, na sha gwagwarmaya wajan cusa wa yara tarbiya tagari, a lokacin da nayi ƙoƙarin hana yara shaye-shaye a makarantar maza da ƙoƙarina aka daina shaye-shaye. Na kasance nice wadda nake kula da ɗakinsu saboda nasiha da nake masu ya kasance sun daina shaye-shayen.
Kamar yadda na yi bincike, wasu lokutan laifin iyaye ne, wasu abokai ne su ka saka su, wasu ‘yan mata ne, wasu kuma vacin rai ne. da dama sune suke bayyana min dalilansu, kuma da taimakon Allah da yawa sai da suka shiryu, su ka daina. Haka a makarantar Mata, na taɓa cin karo da wata yarinya da muke zargin Mata-Maza ce, amma da aka ɗora min alhakin bincike, itama sai muka gano cewa mace ce ba mata-maza ba, kuma itama a lokacin mahaifiyarta sun rabu da mahaifinta sakamakon haka ne yasa iyayen basa kula da ita, sai take mu’amala da yan daba, sune suke kaita makarantar, sune suke mata komai in anyi hutu, kuma a gunsu take rayuwa. Da muka gano haka sai da muka daidaita iyayenta, muka ci gaba da sanya ido akan ta har Allah ya shiga lamarin ta daina. Yanzu haka irin waxannan ɗaliban da yawa daga cikinsu, sun zama manyan mutane, suna aiki a manyan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da jihohi. Ina alfahari da su.

Kin yi aiki a makarantar ‘yayan Fulani makiyaya. A fahimtar ki mene ne matsalar Fulani?
Ni a fahimtata ambar ‘ya’yan Fulani makiyaya a baya ta fuskar ilimi. Kuma ƙarancin ilimin zamani da na arabiyya shi ne yasa bafilace dake cikin daji bai san dokoki ba. Sakamakon haka ko gari suka shigo da abin haka suke karya dokokin ƙasa, ake kamasu, ake cin tararsu. Haka zalika inka ɗauki ɓangaren asibitin mata masu yoyon fitsari, mafi yawansu Fulani ne. Su ne ‘ya’yansu su ka fi fama da ciwon tamowa ba wai don sun fi kowa talauci ba, a’a, sai don suna da ƙarancin wayewar kai. Su ne sukewa ‘ya’yansu mata aure da wuri, suna da ƙarancin shekaru, sannan kuma da yawa daga cikinsu ko sakandire basa gamawa ake masu aure. Saboda haka akwai buƙatar gwamnati ta dawo da tsarin wayarwa da Fulani makiyaya kai ta hanyar amfani da majigi, da kuma sanya tallace-tallace masu ma’ana da za su sauya rayuwar Fulani a gidajan talabijin da gidajen radiyo. Don haka ina kira ga Gwamnatin Nijeriya da ta samar da wasu cibiyoyi da za a riƙa bin Fulani makiyaya har rugagensu, ana gwada masu sana’o’in hannu da zasu dogara da kansu. Domin su Fulani mutane ne masu kaifin basira. 
Ɗaya daga cikin basirar Fulani, ka dubi bafulace da ke kwana a daji, amma ba  arabi ba boko, in yasa shanu a gaba sai yaje har Kamaru da su, ya na tafiya ya na yada zango, ya je ya dawo ba tare da yayi amfani da taswirar ƙasa ba. Amma ɗan boko in ya shahara sai yayi amfani da ‘map’. Ilimin Bafilatani da ya yi yawo da dabbobi ya fi farfesan da ya jima ya na farfesansa. Kuma ko yadda suke magana da dabbobinsu kai kanka kasan akwai ilimi a cikin alamarin. Shanunsu in sun kai ɗari ya san sunan kowacce, kuma in ya yi magana kowacce tasan abinda yake nufi, kuma a dokar daji shanu basa barin wani abu ya cutar da mai kiwonsu, su ne suke ba shi kariya. Haka zalika idan ka duba zai wahala bafilatane ya sayar ko ya yanka uwar gargensu. Suma a shanu akwai shugabansu, kuma sau da yawa shanu su ne suke yiwa masu su bushara da lokacin tashi. 

Me ya fi ba ki sha’awa a rayuwar Fulani makiyaya?
A lokacin da Fulani suke tura ‘ya’yansu daji kiwo, dayawa basa tafiya da abinci, nonon shanun shine abincinsu. Shanun suke kamawa su saka bakinsu kamar ‘ya’yan shanun, sai sun ƙoshi. Amma hakan ya na da haɗari matuƙa. Shan nonon ba tare da an dafashi ba, shine yake sa suke kamuwa da cutar tarin fuka, kasancewar akwai ƙurar daji dake tashi ta lulluɓe nonon, sakamakon haka suke kamuwa da cutar gaha. Duk rashin ilmin abun ne ke jefaru a hatsari.

To, me ya fi ba ki tausayi a rayuwarsu?
Abinda ya fi bani tausayi da takaici ba kamar cin zarafin ya’ya mata. Domin akwai wata rana da na samu labarin wasu mutanen banza sun afkawa wata budurwa ‘Yar Fulani a daji har sukai mata fyaɗe. Da yake suna da yawa sun fi ƙarfin shanun, sai da suka cimma burinsu, har sai da Allah ya kawo wasu manoma, sune su ka kore su, sakamakon ihu da ita yarimyar tayi. Don haka akwai buƙatar a ce Gwamnatin Nijeriya ta yi wata doka da zata hana ‘ya’yan Fulani mata kiwo a Nijeriya

Batun yawan shaqatawa; ƙasashe nawa ki ka je a duniya?
Ƙasashe uku na je; Sudan, kamaru da United Kingdom.

A cikinsu, wacce ƙasa ce ta fi burge ki?
A gaskiya United Kingdom ita ce ta fi burge ni, saboda suna bin dokokin ƙasarsu. Kuma yaransu suna da ƙoƙari wajan sana’a. Wannan ɗabi’a ta yaran su ta sa da na dawo gida, na zaburar da ‘ya’yana. Sai dai yadda muke fama da yan shaye-shaye, suma haka suke fama da su, amma fa su na su a killace suke. Kuma su gwamnatin ta na rage yawan adadin abinda suke sha, a hankali, a hankali har su daina sha. Saɓanin nan gida Nijeriya.

Daga cikin waɗannan ƙasashe da ki ka je, wace ƙasa ce ta ke da tsari irin na Nijeriya?
Sudan ce take da tsari irin namu, amma fa su suna da matsala irin tasu, saboda babbar matsalarsu ƙarancin ruwan sama. Basa samun ruwan sama kamar namu. Mu kuwa Allah ya wadatamu da ruwan sama da bishiyoyi da furanni kala-kala. Sudan kuwa ƙasa ce da jama’arta suke fama da talauci matuƙa. Suna da tsadar rayuwa, ba su da abinci sai shayi. Zai wahala kaje Sudan kaga runbu ko siton ajiyar abinci a gida. Ɗan kasuwa ko ma’aikacin gwamnati inya ɗauki albashi ko inya dawo daga kasuwa gabaɗaya yake miqawa matarsa kuɗin da ya samu. Kuma a Sudan aure yana da tsada ba kowa ne za ka gan shi da mace sama da ɗaya ba. Mafi yawansu mata ɗai-ɗai sukedasu. Wannan shayin da ka ga suna sha bawai wadata bace, talauci ne. Basa sayan shinkafa ko masara buhu su ajiye agidajansu, komai sacis-sacis suke saye, domin ko akantinan su ba za ka ga kaya a shago fal ba kamar yadda kasuwarmu suke ajiyewa ba. A gaskiya ni dai da na ga irin yadda suke rayuwa, bana sha’awar irin rayuwarsu, domin da na ga yadda suke rayuwa daga wani fale-falen biredi da agawa, sai nace ashe Nijeriya cikin jin daɗi muke, domin talakan Nijeriya shine mai kuɗin Sudan.

Ko a can Sudan su ma su na yi wa ‘ya’yansu auren wuri?
Tabɗijan! Ai aure a Sudan abu ne mai wahala saboda tsadar auren, domin namiji shine yakeyin komai, iyayan mace basa sayan komai. Kuma iyaye suna kai mace gidan miji ne daga ita sai kayan jikinta, mafi yawanci Mata suna kaiwa shekara hamsi kafin ayi masu auren fari. Kuma zai wahala ka ga aure ya mutu. Kuma duk wadda yayi aure, in zai sake aure ita ma sai dai ya gina mata wani gidan. Bai isa ya haɗasu wuri ɗaya ba. Haka idan aurensa ya mutu da matar, sai dai ya fice ya bar mata gidan, ma’ana gida ya zama nata. Haka dokarsu take ko ta haihu da mijin ko bata haihu ba.

A Sudan ta ya ake gane mai aure da marar aure?
A na gane mace mai aure ne kawai ta ƙunshin lalle. Duk matar da ka ga bata da ƙunshi budurwa ce, ko kuma bazawara saboda doka ce a can mace in bata da miji bata da ikon yin lalle.

Mene ne kiran ki ga ‘yan’uwanki Mata musamman ta fuskar ilimi?
Mata su dage wajan neman ilimin addini da na zamani, domin matuƙar Mata suka bada ƙoƙari wajan neman ilimi, al’ammura zasu gyaru sosai a faɗin Nijeriya. Mata a matsayinsu na iyayen al’umma, ilimin su yafi na maza amfani a cikin al’umma, domin sau da yawa matsalolin da suke faruwa suna faruwa ne sakamakon ƙarancin ilimin iyaye mata, saboda haka ya zama dole iyaye mata su tashi tsaye wajan ilimin rayuwa da na addini.

Ta fuskar lafiya, mene ne shawarar ki ga ‘yan’uwan ki mata musamman Fulani da suke ruga?
Shawarata su riƙa zuwa asibiti kuma idan aka ba su magani, su riƙa amfani da shi musamman maganin maleriya. Idan an ba su su riƙa bai wa ‘ya’yansu, domin sai da qwararru suka yi nazari akan maganin sannan aka ba su, ba haka kawai aka ba su shi ba. Amma sau da yawa wasu idan an ba su ba sa bai wa ‘ya’yansu, hakan ba ƙaramar illa ba ce kansu da kuma ‘ya’yansu. Haka zalika Ina kira ga ‘yan’uwana Fulani da su riƙa gina banɗakuna a gidajansu domin rashin banɗakuna da yin bahaya a daji shine yake haifar da cututtuka irin su; amai da gudawa, sakamakon shan ruwa marar tsafta da yake ɗiban bahayar da mu ka yi a waje, ya ke kai wa ruwan da mu ke sha.

Hajiya, mun gode matuƙa. 
Ni ma na gode sosai.