Ya kamata malamai su riƙa yi wa bakinsu linzami

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ba da jimawa ba ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Muhammad Abubakar na lll ya yi wani kira ga malaman addini da masu wa’azi su yi hattara da irin wa’azozin da suke yi a kan minbarori a masallatai da coci coci, sakamakon yadda wasu malaman ke amfani da matsayin su na masu faɗa a ji suna tunzura jama’a da yaɗa kalamai na ɓatanci da ƙiyayya a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Ba wannan ne karon farko da Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi irin wannan kiran ba ga malaman addini da sauran ‘yan Nijeriya dangane da yadda ake sakin baki ana faɗar maganganu na ɓatanci da cusa gaba da ƙyamar juna a tsakanin mabiya da sauran abokan zama, masu bambancin addini, ƙabila da siyasa.

Abin tambaya a nan shi ne, shin waɗannan kiraye kirayen da ake yi yana samun karvuwa a wajen malamai magada Annabawa ko pada pada da ke jagorantar miliyoyin ‘yan ƙasa a ɓangaren addini, waɗanda ke musu kallon fitilu kuma madogara a dukkan harkokin su na rayuwa, da na neman tsira a wajen Ubangiji.

’Yan Nijeriya, waɗanda duniya ta shaida cewa su mutane ne masu haƙuri da rayuwa da kuma kishin addini, sun kasance masu nuna tsananin biyayya da sallamawa ga al’amarin malaman addini, da suka yi imanin ilimin su da tsarkin zuciyar su ko kusancin su da Ubangiji ya ba su wani matsayi maɗaukaki na sanin gaskiya da fahimtar duk wani al’amari na rayuwa. Don haka duk wata magana da ta fito daga bakin malam ko faston da suka gamsu da shi kuma suke yi wa biyayya to, babu kokwanto a kanta.

A irin haka ne ake samun mabiya su zama masu aiki kai tsaye da kowacce irin fatawa ko fahimta da ta fito daga jagoransu ko da kuwa ta saɓa da abin da ƙwararru ko mafi yawan jama’ar ƙasa suka yi amanna a kai, kamar game da abin da ya shafi kiwon lafiya, tsaro, tattalin arzikin ƙasa da siyasa. Saboda imanin da tarbiyyar addini ta ɗora mu a kai cewa, kowanne al’amari yana da mahangarsa a cikin addini, kuma matsayar addini ita ce gaskiya. Za mu iya tunawa da yadda a shekarun baya aƙidar Boko Haram ta samu karɓuwa a wajen wasu ‘yan Nijeriya, ciki har da waɗanda ake yi wa kallon masu ilimi ne da wayewa ta boko. Sannan da irin yadda aka yi ta sa toka sa katsi da wasu malamai da fastoci game da inganci ko rashin ingancin matakan yaƙi da yaɗuwar annobar Korona ko rigakafin cutar da ake ta kira ga jama’a su karva.

Mun sha ji da ganin yadda wasu masu wa’azi da ake danganta su da addinin Kirista suke yaɗa maganganu na tunzurawa da ƙyamar wani ɓangaren al’umma, sakamakon bambancin addini, ɓangaranci, siyasa, ko ƙabila. Yadda za ka ga mai wa’azi ya dage yana gayawa mabiyansa ko almajiransa wasu abubuwa da sam ba daidai ba ne, ko kuma sun savawa hankali da bincike na masana. Amma zai yi amfani da tasirinsa a wajen su, ya nuna musu cewa, abin da ake ƙoƙarin ɗora ‘yan ƙasa a kai ba daidai ba ne, wani makirci ne ko yaudara ce don a cutar da su, saboda a nisanta su da addini ko gurɓata makomar su.

Amfani da wuraren ibada ko cibiyoyin ilimi da wasu malaman addini suke yi domin yaɗa manufofin su na ƙabilanci, ƙyamar wani addini ko wata aƙida, mahangar siyasa da bambancin fahimta, babban kuskure ne, saboda a lokuta da dama abin da suke ƙoƙarin ɗora mabiyansu a kai bai inganta ba, ko ilimi bai tabbatar da shi ba, ko kuma akwai fuskoki daban-daban na fahimtar ƙalubalen da ake taƙaddama a kai daga hujjoji da dama. Amma saboda ƙarancin fahimta, ko jahilcin wani fage na ilimi, ko ma dai hassada irin ta wasu malamai da son zuciya ta ‘yan adamtaka, sai ka ga an gwara kan mabiya, da sauran ‘yan ƙasa ana ta muhawara, aibata juna ko amfani da wasu maganganun malamai a matsayin hujja ta ƙin juna ko shiryawa juna makirci.

Ana samun wasu masu iƙirarin cewa su mutanen Allah ne, masu gaskiya ne, da tarin ilimi, amma ayyukan su da kalaman su yana nuna akasin haka. Yayin da sau da dama suke amfani da inda ra’ayin mafi akasarin jama’a, musamman mabiyansu, ya karkata ne ko abin da ya fi ɗaukar hankalin ‘yan ƙasa, su bayyana tasu fahimtar da za a ɗauka a matsayin ita ce daidai ko ita ce ta dace da bin Allah, ko da kuwa akwai kuskuren fahimta ko son zuciya da ra’ayi a kai.

Bai kamata a samu malamin addini, fasto ko Rabaran yana ƙoƙarin yaɗa saƙonnin ƙiyayya ko raba kan jama’a ba, domin suna da saɓanin fahimta a keɓance ko a ƙungiyance da wasu ba. Ko kuma a samu malami dumu dumu cikin maganganu irin na adawa da gwamnati, ko tozarta wasu ma’abota addini ko masu faɗa a ji, ko zuga magoya baya ƙin yin biyayya ga wasu manufofin gwamnati ko abin da ya shafi tsaro, kiwon lafiya ko zaman tare tsakanin addinai da ƙabilu mabambanta. Hakan yana da haɗari sosai ga al’amarin zamantakewa, da mutuncin su kansu malaman da kimar su a cikin al’umma. Mun sha ganin inda malami da ke taƙama da gadara da magoya baya ke ganin ya fi ƙarfin doka ko gwamnati, a ƙarshe ya zama abin kyara da tsangwama, daga ɓangarori daban-daban. Mun ga inda alaƙa da ‘yan siyasa ta jefa wasu malamai da ake ganin su da kima da martaba, cikin zargin cin kuɗin makamai da sauran su. Taurin kan wasu malamai saboda ganin yawan magoya baya ya jefa ƙasa cikin ruɗanin siyasa da tsaro, wanda har yanzu ake kokawa da shi.

Manufar wannan rubutu shi ne nuna goyon baya ga kiraye kirayen Mai Alfarma Sarkin Musulmi, miƙa nasiha ta ga malamai magada Annabawa, iyayen al’umma, don su ƙara kare mutuncin su da kimar su a idon duniya, tsare martabar malanta da ilimi, samar da haɗin kai tsakanin malamai da hukumomi, domin tafiyar da ƙasa ƙarƙashin fuska guda, ba tare da raba kan al’umma ba.

Kira na ga malamai shi ne su kaucewa, zaƙewa wajen gabatar da wa’azozin su, domin gudun kada son zuciya ko ƙoƙarin jan ra’ayin jama’a da magoya baya ga duk wani abu da suke ganin zai iya ɗaga darajar su ko wani abu da suke so, ya zama shi ne ya fi tasiri a cikin karantarwar su, hakan kuskure ne sosai.

Shi ya sa tsohon ɗan jarida kuma tsohon ministan shari’a Cif Tony Momoh a wata muƙala da ya gabatar a wani babban taron ‘yan jarida na ƙasa da aka gudanar a Legas a shekara ta 1995, ya ja hankalin malamai da marubuta cewa, ba burgewa ba ce marubuci ko malami ya yi rubutu da zai ɗaga darajarsa, ko ra’ayinsa, kambama wani tunani da yake so ya gina mutane a kansa ba, hakan ba nasara ba ce a kansa ko al’ummar sa ba, domin yanayi yana iya canjawa.

Lokaci ne da hukumomi za su ƙara sa ido kan ɓangaren addini da cibiyoyin ilimi, domin tantance baragurmin masu wa’azi da malamai, da ke amfani da addini suna cusa wa matasa gurguwar fahimta, da aƙidu masu haɗari ga tsaron ƙasa, da zamantakewar al’umma.

Malamai su ma ‘yan qasa ne da ke ‘yancin faɗar albarkacin baki da kasancewa a cikin kowacce ƙungiyar addini ko majami’a da suka ga ya dace da fahimtar su, matuƙar ba zai zama haɗari ga ci gaban ƙasa da haɗin kan al’umma ba. Yana da muhimmanci mu ba su shawarwari a duk lokacin da muka ga dacewar hakan domin gyara yadda tafiyar da al’amuran ƙasa za su zama da sauƙi da haɗin kai. Su ma mutane ne masu iya yin daidai ko kuskure, amma kusancinsu da Allah yana sa su zama masu tsantseni da kiyayewa. A duk inda aka lura akwai buƙatar ba da shawara, yana da kyau a yi hakan, domin cigaban mu ne baki ɗaya.

A kundin tsarin mulkin qasa sakin layi na huɗu, an yi bayani game da haƙƙoƙin da ɗan ƙasa yake da shi, na faɗin albarkacin bakin sa ko zama a duk inda ya ga dama, ko haɗin kai da duk wata al’umma da ya yi ra’ayi, da yaɗa wata manufa da take da tasiri a rayuwar sa, wannan bai ba shi dama da zai zama sakaka ba, domin kuwa an sanya wani tarnaqi da zai yi masa linzami, don kaucewa shiga haqqin wani, wasu ko dokokin ƙasa. Saboda kuwa inda damar sa ta tsaya, a nan ta wani ta fara.

Yana da kyau gwamnati ta riqa shirya taruka na faɗakarwa da qarawa juna sani lokaci zuwa lokaci ga malaman addini, ƙarƙashin Majalisar Kula da Al’amarin Addini, kamar yadda a baya take ƙoƙari. Jami’an tsaro da hukumomin gwamnati su riƙa shiryawa malamai horo da tunatarwa game da manufofin gwamnati da tsare tsaren ƙasa, don haka ya taimaka wajen qara samar da kyakkyawar fahimta a tsakanin al’umma baki ɗaya.

Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya a ƙasarmu Nijeriya.